Tilasta Wa ’Yan Takara Ba Dimokuradiyya Ba Ne –Hon. Wadada

Honarrabul Ahmed Aliyu Wadada (Barden Keffi) tsohon dan Majalisar Tarraya ne kuma daya cikin jerin wadanda suka nuna sha’awarsu na zama gwamnan Jihar Nasarawa a shekarar 2019 a karkashin jam’iyya mai mulki, APC. A kwanannan ya kai ziyarrar gaisuwa ga mai martaba sarkin Lafia wanda ya dawo daga kasar waje, kana daga bisani ya karasa inda zai kasance ofishinsa na yakin neman zabe. Wakilin LEADERSHIP A YAU Abubakar Abdullahi ya yi kicibis da shi inda suka tattauna game da batuttuwan siyasa da sauran lamurran da suka shafi kasa. A sha karatu lafiya:

Ka kasance na gaba-gaba cikin wadanda suka nuna sha’awar yin takarar gwamnan Jihar Nasarawa, to amma sai ga shi a kwanan nan labari ya bazu ciki da wajen jihar cewa ungulu za ta koma gidanta na tsamiya ma’ana za ka koma Jam’iyar PDP, ina gaskiyar wannan batu?

Wannan zancen abin dariya ne kuma labari ne da ban san da shi ba. Bari ma ka ji yadda kai ka fadi zancen ya ma fi kyau da yadda ake yayata labarin. Wadanda suke yada labarin suna cewa ne tuni na rigaya na rubuta takarda zuwa ga shugaban jam’iyar PDP na gundumata ina mai sanar da shi aniyata ta komawa tsohuwar jam’iyata, wato PDP. Wannan labarin karya ce tsagwaranta, babu wani abin da ya faru kamar haka sannan babu wani abu mai faruwa kama da haka nan kusa. Na kasance dan jam’iyar PDP na wani lokaci kuma na canja sheka daga cikinta zuwa jam’iyar APC bisa wani dalili, sannan babu wani abu da ya baci a jam’iyar APC a yau da zai sa ni yin tunanin barin ta in sake koma jam’iyar PDP. Sai dai wasu suna ganin yin hakan siyasa ne amma ni a gare ni ba siyasa ba ne. Siyasa aba ce da ta kamata ta rika tafiya da gaskiya a kowane bangare, kenan idan haka ne bai kamata a rika tafiyar da siyasa da karya ko yaudara ba.

Ni dai abubuwan da na lura suke tsoratar da wasu mutane suke yada karya a kaina su ne, tarihin siyasata da irin jama’ar da suka rungumi tafiyata.  Wasu cikin jam’iyar APC sun ce me za sa Wadada ya nemi takara a jam’iyyar? Yaushe ya shiga jam’iyyar? Irin wadannan su ne ba su ma san mene ne kundin tsarin mulkin jam’iyar APC ya kunsa ba. Kundin tsarin mulkin jam’iyar APC ya ce duk wanda ya shiga jam’iyar APC a yau ba ma gobe ba ‘yancinsa daidai yake da na wanda ya kafa jam’iyar.

Domin duk wanda ya raina ko kaskantar da komawana jam’iyar APC  kenan ba shi da tarihin yadda aka kafa jam’iyar. Domin idan ka duba tarihin jam’iyar APC da yadda aka kafa ta ba za ka yi watsi ko raina irin gudumawar da bangaren jam’iyar PDP na PDP2 ya bayar ba aka kafa jam’iyar.

Ni a bangaren PDP2 ba wai dan jam’iyya ne ba kawai a’a, ni ne sakataren kudi na kasa na bangaren. To kenan Wadada ya bada gudumawa wajen kafa jam’iyyar APC. Domin haka na shigo gida, kowa ya saki jikinsa, ni cikkakken dan jam’iyyar APC ne,  mai yi mata biyayya da sadaukarwa kuma zan yi takarar kujerar gwamnan Jihar Nasarawa a karkashinta.

 

Wane irin yakini kake da shi cewa jam’iyyar APC za ta samar da kyakkyawan yanayin da zai sa hakarka ta cimma ruwa?

Ina da kyakkyawan yakini saboda ina kyautata zaton APC ta yi gaskiya da adalci. Mene ne ma kyakyawan yanayin a tsarin dimokuradiyya? Kyakyawan yanayi shi ne batun jama’a kuma na samu jama’a. Domin haka ni a gare ni akwai kyakkyawan yanayi fiye da lokutan baya.  Ina tuntunbar jama’a, ina mu’amala da kuma tattaunawa da jama’a, sannan kwamitin da na kafa yana kewaya jihar yana zantawa da mutane kuma babu wani dan takarda a Jihar Nasarawa da ya nuna kansa ga mutane kama na. Babu wani da ya ce kar in shiga wani yanki domin yada manufata. Za mu yi wa jama’ar Jihar Nasarawa abin da ya dace idan Allah ya kai damo ga harawa.

 

Mu kaddarra idan jam’iyar APC ta ce  maka ka janye kudurin takararka ka bai wa wani daman, za ka ci gaba da zama a jam’iyyar ko kuwa ficewa za ka yi ka sauya sheka?

Idan hakan ya kasance sai in ce babu dimokuradiyya a APC kuma ba ta dace ta wanzu a matsayin jam’iyya ba. Kar wani ya dube ni ya ce in janye wa wani, bisa wane dalili? Wannan ba dimokuradiyya ba ce. Kamar yadda na sha fada, duk da dai ban rike kowa a zuciyata ba, amma ni ba mai goyon bayan mika damar tsayawa takarata ga wani mutum ko yanki ba ne, wato ‘zoning’, domin babu dimokuradiyya a haka. Ban san dalilin da wani zai dube ni Wadada a yau ya ce in janye takarata, in janye wa wani mutum? Bisa wane dalili kenan? Fada min dalilin da zai sa in janye wa wani? Shin mutumin da ake so in janye masa ya fi ni ne?

 

Tun da dai ka karyata wannan rade-radin, wane sako kake da shi ga masoyanka?

Ba ni da wani sako ga masoyana saboda suna da masaniya ba wai kawai ina jam’iyar APC a yau a’a, ni cikkakken dan jam’iyya ne mai biyayya da sadaukarwa gare ta. Ga masu yada jita-jita ko zancen da ba shi ne ba, ina mai kira a gare su da su janye labarin da kuma canja halayensu na karya da yaudara su kuma zo su shiga siyasar cigaba. Wadada bai da aniyar barin jam’iyar APC, ina cikinta daram, dakam.

 

Idan mun kauce wa batun siyasa, mutane na bangare kasar nan na ikirrarin a raba kas,. Me za ka ce kan haka?

Da farko ban yarda da a raba kasar nan na. Idan ka duba yanayin yankuna da tsare-tsaren tattallin arziki da zamantakewar ‘yan Nijeriya tun kafuwarta,  an yi mu ne mu zauna tare. To amma hakan bai hana duk wanda yake ganin an yi masa ba daidai ba ya bayyana. Domin haka duk yankin kasa da ke ganin an saba masa, dimokuradiyya ce ai, yankin ya yi kuka kan ba daidai ba da aka yi masa. Sannan yin hakan ya kasance ya bi tsarin dokokin zamanmu na tarraya.

 

Wane tsokaci kake da shi kan jawabin da y buhari ya yi wa yan kasa kwannan nan.

Ban ga wani abin rashin fahimta ko yin cece-kuce ba a cikin jawabin Shugaban kasar. Shugaban kasa ya kasance a zaune a kasar waje domin jinyar rashin lafiya na kwanaki sama da dari kuma ya dawo gida. Shugaba Buhari ya zabi ya yi Magana a kan batuttuwan da ‘yan kasa ke ta cece-kuce a kansu irin su tsaro da furta kalamun nuna kiyayya da tada hankula a fadin kasa, kuma babu shakka hakkinsa ne a matsayinsa na shugaban kasa ya janyo hankulan ‘yan kasa kar su rika aikata abubuwan da za mu kara kawo bambance-bambance a tsakaninmu.

Kan batun tsaro kuwa abu ne da ke zaman hakkin kowa. Jawabin shugaban kasa da zai kasance bai kammalu ba idan bai tabo batun tsaro ba. Wadanda ke tunanin Shugaba Buhari bai yi magana kan wasu batuttuwan da suke tunanin ya kamata ya yi,  bai kamata mu zaci cewa Shugaba Buhari zai fadi komai a rana daya daga dawowarsa ba.

Wasu na cewa shugaban ya ce wani abu game da batun bukatar sauya fasalin kasa. Sauya fasalin kasa ba haki ne na shugaban kasa ba, hakan ya wucce kansa. Akan gudanar da sauya fasalin kasa ne a inda akwai bukatar yin hakan kuma kan batun an samu bambanci na masu so da marasa son hakan.

Shugaban kasa ba zai tilasta wa ‘yan kasa abin da ba shi suke bukata ba. Shi shugaba ne bisa zabi da ‘yan kasa suka masa kuma batun sauya fasalin kasa ko akasin haka abu ne da baki dayan ‘yan Nijeriya ne za su yi shi ya sa ma Majalisar Dokoki da Majalisar Koli su kasance bangarorin da ka iya tattaunawa kan batun.

Exit mobile version