Tilasta wa kamfanoni masu sarrafa kayan amfani gona ne kawai zai rage tsadar amfani gona
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Munkaila Garba, shugaban kunkiyar manoman Masara (MAAN) na kasa reshan Jihar Kano lokacin da ya ke ganawa da manema labarai kan batun bude iyakokin Nijeriya, ya ce a matsayinsu na manoma basa goyon bayan bode iyakokin Nijeriya domin abu ne da zai zama koma baya da cigaban noma da kamfanoni, kuma koma- baya ga tatalin arzikin kasa, domin a ce kasa bata dogaro da kanta sai da wata kasa wannan koma-baya ne don haka akwai bukatar a yi taka-cancan kuma a lura da kyau a yi abin da zai ciyar da kasarmu gaba ba baya ba a cewar shugaban MA
AN na Kano.
Har’ila yau ya ce kamfanoni masu sarrafa kayayakin amfanin gona kamar masara shinkafa dawa alkama, gyada, wake, da dai sauran kayan bukatu na yau da kullum da suke tsada ba don rufa iyakoki ba ne, a’a kamfanoni ne da suke bin Manoma a gonaki tun da danyar Kaka suna saye kayan amfani gona, wannan shi ne yake kawo tsada da karancin amfani gona.
Amma idan Gwamnatin Tarayya ta yi doka ta ce tilas ko wanne kamfani sai ya Noma kayan da zai sarafa ko da kashi 70 ko 50 cikin 100 ko kuma ya sa kunkiyoyi irin na mu su noma masa to yin haka ne zai sa a samu saukin kayan amfani gona a Nijeriya.