Daga El-Mansur Abubakar, Gombe
Hajiya Harirah Abdulsalam, Mace ce yar rajin kare yancin Mata ta koka kan yadda wasu Mazaje ke yaudarar da Mata suke hana su yin aure kuma su basa aurensu.
Harirah Abdulsalam, ta bayyana bakin cikin ta kan hakan a lokacin da take zantawa da jaridar Leadership A Yau inda tace yana da kyau a samar da wata doka a ƙasar nan ta tilastawa Mazaje auren Matan da suke yaudara.
Tace wasu Mazan sun mayar da Matan waje waɗanda ba Matan su na cikin gida ba tamkar ba Mata ba domin a kullum burin su shi ne su ga sun sami hanyar da za su keta musu ‘yanci su kuma ketare su barsu.
A cewar ta irin haka ne yake hana wasu Matan yin aure saboda sun sa rai sun sami Mijin aure ashe mayaudari ne kuma ko anyi auren baya jimawa saboda da tsakani da Allah ya aure ta ba.
Daga nan sai Hajiya Harirah Abdulsalam, ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da hukumomin kare yancin ɗan adam da sauran jami’an tsaro da za su samar da doka wacce za ta tilasta Namiji auren Matar da ya yaudara kuma a sa doka na hana saki har sai da ƙwaƙwaran dalili.