Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
Ɗan majalisar wakilai na tarayya, Hon. Gudaji Kazaure, ya bayyana cewa, tilastawa Musulmi ya aiwatar da tsarin ƙayyade iyali tamkar tirsasa shi ne a kan ya aiikata saɓon Allah, ya na mai cewa, Manzon Allah (SAW) ya umarci Musulmi da su yi aure su hayayyafa, domin zai yi alfahari da yawansu ranar alƙiyama, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.
Ɗan majalisar, wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi daga jihar Jigawa, kafar yaɗa labaran ta ruwaito shi ne ya na bayyana a hakan a wani hoton bidiyo a yayin da ya ke ƙalubalantar ƙudirin da ke neman a kafa dokar ƙayyade iyali a Nijeriya.
Kazaure ya yi kira ga kakakin majalisar da ya yi watsi da dokar, domin ta saɓa ta kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda ya bai wa kowa damar bin addininsa ba tare da tsangwama ba matuƙar bai shiga haƙƙi ko ’yancin wani ba.