Tinubu Da Ganduje Suka Fi Dacewa Da Mulki A 2023, In Ji TPN

Tinubu Ganduje

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Shugaban kungiyar magoya bayan Tinubu (TPN) reshen Jihar Kano, Muhammad Tajo, yace babu kamar Tinubu a 2023,Tajo ya kuma yi kira ga Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, da ya amince ya nemi mataimakin shugaban kasa.

Yace Tinubu da Ganduje sun dace kuma sun cancanta su jagoranci ‘yan Nijeriya a zaben Shekara ta 2023. Jagoran siyasa a Jihar Kano kuma shugaban kungiyar magoya bayan Tinubu a Jihar (TPN), Muhammad Tajo Nagoda, ya bayyana cewa babu wanda ya dace ya dare mulkin shugabancin kasar nan a zaben Shekara ta 2023 sama da jigon APC, Bola Tinubu.

Shugaban ya fadi haka ne a karshen mako da ya gabata yayin da yake Tattaunawa da manema labarai a Kano, ya kuma yi kira ga Gwamna Ganduje na Jihar Kano da ya amince ya nemi mataimakin shugaban kasa.

Tajo ya bayyana Bola Tinubu a matsayin mutumin da ‘yan Nijeriya suke bukata a halin da ake ciki.

Yace: “Gare mu ‘yan kungiyar TPN a Kano, mun yi imanin cewa akwai bukatar ingantaccen shugaba a 2023, shugaban dake da kwarin guiwar fuskantar duk wani kalubalen siyasa da zai iya tinkarar sa.”

“A wurin mu wannan shi yafi dacewa da Nijeriya a zaben 2023 kuma ba kowa bane illa Alhaji Bola Ahmed Tinubu. Mu anan arewa bamu da wanda ya fishi dacewa.”

Tajo Ya roki Ganduje ya amince ya nemi nataimakin Tinubu, da yake kare bukatarsa ta Ganduje ya nemi mataimakin shugaban kasa, Tajo ya yi watsi da banbancin kabila da addini da wasu ‘yan Nijeriya ke maida hankali a akai.

Yace: “Duk masu tsayawa duba kabila da addini fiye da kwarewa da cancanta wanda muka gani ga Tinubu da Ganduje, to ba su son gaskiya wajen zaben shugabanni nagari.”

Exit mobile version