Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a sake duba dabarun kadarorin asusun fansho domin ba da damar zuba jari a ɓangaren man fetur da iskar gas a Nijeriya.
Shugaban kasa, Tinubu, wanda ya kaddamar da tashar fitar da ɗanyen mai ta ‘Green Energy International Limited (GEIL)’ a Otakikpo, jihar Ribas, a ranar Laraba, ya jaddada irin gagarumar ribar da za a iya samu idan aka zuba hannun jarin a masana’antar ta mai.
Tashar Otakikpo ita ce tasha ta farko ta ‘yan Nijeriya wacce za ta fara fitar da ɗanyen mai kuma ita ce sabuwar tasha ta farko da aka gina a ƙasar bayan shekaru hamsin da suka gabata.
Shugaban wanda ya samu wakilcin Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, Shugaban kasar ya ce tuni gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da al’ummar Ogoni domin magance duk wata matsala da za ta iya kawo cikas ga tashar domin fara samar da ɗanyen mai.