Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da tallafin Naira 250,000 ga ƙananan ‘yan kasuwa da matsakaitan masana’antu (MSME) da suka nuna bajinta a yayin Taron Ƙanana da Matsakaitan Masana’antu na Ƙasa (Expanded National MSME Clinic) da aka gudanar a Katsina.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya sanar da hakan yayin ƙaddamar da taron karo na tara na shirin, wanda aka shirya don tallafa wa ƙanana da matsakaitan sana’o’i da kuma farfaɗo da tattalin arzikin al’umma.
- Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi
- Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki
Shettima ya bayyana cewa an samar da shirin ne domin kawo hukumomin gwamnati kusa da masu sana’a da kuma karfafa fasahar ƙirƙire-ƙirƙire, samar da ayyukan yi, da sauƙaƙa samun rejista ko tallafi daga cibiyoyi kamar CAC, NAFDAC, SMEDAN, da Bank of Industry.
Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda ke bai wa ’yan kasuwa rancen har zuwa Naira miliyan 5 da kaso tara cikin ɗari (9%) a matsayin kudin ruwa, da kuma Naira biliyan 50 a ƙarƙashin shirin Shugaba kasa Bola Tinubu da ke bai wa ƙanana ’yan kasuwa tallafin kuɗi kyauta bisa wasu sharuɗɗa domin bunƙasa kasuwanci (Presidential Conditional Grant Scheme) da ke ba da tallafin Naira 50,000 ga ’yan kasuwa miliyan ɗaya a fadin kasar.
Haka kuma, gwamnatin ta samar da Asusun Tallafin Masana’antu daga Gwamnati (Manufacturers Fund) na Naira biliyan 75 don tallafa wa masana’antu wajen rage tsadar samar da kayayyaki da sufuri.
Mataimakin shugaban ƙasan ya ce sama da ’yan kasuwa 39,000 a jihar Katsina sun amfana da shirye-shiryen gwamnatin tarayya, inda aka raba Naira Biliyan 2.5 a matsayin tallafi da rance mai rangwame.
A ƙarƙashin shirin RAPID, Shettima ya ce ’yan kasuwa 23 daga yankunan karkara sun samu fiye da Naira Miliyan 112 don faɗaɗa kasuwancinsu. Ya kuma yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa kafa KASEDA, yana mai cewa Katsina na zama cibiyar ci gaban masana’antu, noma, da kasuwancin yanar gizo a Arewacin Nijeriya.














