A daren yau ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta makonni uku a Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an ƙasa da ƙasa don inganta dangantakar Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki.
Jirgin shugaban ya sauka ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja da misalin ƙarfe 9:50 na daren ranar, inda ya samu tarɓa daga manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban Ma’aikatan Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila; Mai Ba da Shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu, da Ministan Birnin Tarayya, Barrister Nyesom Wike.
- Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman Zamani: Jigawa Ta Baje Kolin Aikin Noma A Abuja
- Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya
Shugaba Tinubu, wanda yayi tafiya tun a ranar Laraba, 2 ga Afrilu, ya fara ziyarar ne a Paris, Faransa, kafin daga bisani ya tafi Landan, Birtaniya.
Duk tsawon lokaci da yake wannan tafiya a Turai, shugaban ya ci gaba da tuntuɓar manyan jami’an gwamnati, yana bayar da umarnin aiwatar da muhimmancin al’amuran ƙasa, musamman ma na tsaro.