Tinubu Ya Nada Ribadu Da Wasu A Matsayin Masu Ba Shi Shawara
  • English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Nada Ribadu Da Wasu A Matsayin Masu Ba Shi Shawara

bySadiq
2 years ago
Ribadu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada masu ba shi shawara kan harkoki daban-daban ciki har da Mallam Nuhu Ribadu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na musamman.

Wata sanarwa da Abiodun Oladunjoye, daraktan yada labarai a fadar shugaban Najeriya ya fitar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da nade-naden da suka haɗar da Mista Dele Alake a matsayin mai ba da shawara kan harkar ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare.

  • Yariman Bakura Ya Taya Akpabio Murnar Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10
  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Daliban Jami’ar Jos 7

Akwai kuma Mallam Ya’u Darazo a mukamin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da hulda tsakanin gwamnatoci.

Haka zalika, Tinubu ya amince da nada Mista Wale Edun a matsayin mai ba da shawara na musamman kan manufofin kudi.

Akwai kuma mai ba da shawara ta musamman kan harkokin makamashi, inda Tinubu ya naɗa Misis Olu Verheijen.

Ƙarin masu bayar da shawarar har da Mista Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudin shiga.

An kuma naɗa Dokta Salma Ibrahim Anas a mukamin mai ba da shawara ta musamman a fannin kula da lafiya.

Sai kuma Mista John Ugochukwu wanda aka nada mai ba da shawara na musamman kan harkokin masana’antu, kasuwanci da zuba jari.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa
Manyan Labarai

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Manyan Labarai

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026

October 7, 2025
Next Post
Ana Baje Kolin Litattafai Daga Kasashe Da Yankuna 56 A Beijing

Ana Baje Kolin Litattafai Daga Kasashe Da Yankuna 56 A Beijing

LABARAI MASU NASABA

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version