Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta gudanar da sauye-sauye masu muhimmanci, inda ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar za ta rasa muhimmanci idan ba ta magance manyan ƙalubalen duniya ba.
A jawabinsa a babban taron UN, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gabatar, Tinubu ya nemi a bai wa Nijeriya kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Kakkaɓe Masu Amfani da Takardun Bogi a Ma’aikatunta
- Collins Whitworth Zai Kafa Tarihin Shiga Kundin ‘Guinness World Record’ Tare Da Goyon Bayan Indomie
Ya nemi a yi gyare-gyare a tsarin kuɗaɗen duniya, a bai wa Afirka ribar albarkatun ƙasa yadda ya kamata, tare da ɗaukar matakin cike giɓi a fasahar zamani da Intanet.
Tinubu ya kuma nuna goyon bayansa ga mafita a ƙasashe biyu tsakanin Falasdi5nu da Isra’ila.
Ya bayyana cewa cewa Falasɗinawa suna da ‘yanci da mutunci kamar sauran bil’adama.
Ya ce zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai tabbata ne kawai idan aka tabbatar da adalci.
Shugaban ya jaddada irin gyare-gyaren tattalin arziƙin Nijeriya, ciki har da cire tallafin man fetur da sauya dokokin musayar kuɗi.
Ya ce matakan suna da tsauri, amma dole ne a ɗauke su domin samar da ci gaba mai ɗorewa.
A kan tsaro, Tinubu ya ce yaƙin da ta’addanci ba wai da bindiga kaɗai ake cin nasara ba, sai da ra’ayoyi da ɗabi’u waɗanda ke haɗa al’umma.
Ya kuma jaddada aniyar Nijeriya ga zaman lafiya, ci gaba, da kare haƙƙin ɗan Adam, inda ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi canje-canjen da za a iya gani, tare da gargaɗin cewa idan ba haka ba, ƙungiyar za ta zama mara tasiri.