Shugaba Bola Tinubu ya shirya taron sasantawa tsakanin ministan Abuja Nyesom Wike, da gwamnan Ribas Siminalayi Fubara, da wasu ‘yan majalisar jihar a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis da daddare.
Taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin siyasar da ya haifar da ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers.
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Nijeriya Ta Lalata Haramtattun Matatun Mai 5 A Ribas
- Dakataccen Gwamnan Ribas Ya Dawo Daga Hutun Makonni Biyu A Kasar Waje
Majiyoyin fadar sun bayyana cewa Shugaban ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da su zauna lafiya domin amfanin jihar.
A ranar 19 ga Maris, Shugaban ya ayyana dokar ta-baci a Ribas bayan tarzomar siyasa, inda aka dakatar da gwamna da mataimakinsa na tsawon wata shida, sannan aka sanya majalisar jihar ƙarƙashin kulawar tarayya.
Ana sa ran taron zai zama tamkar wani ginshiƙin na janye dokar ta-baci bayan cikar watanni shida a watan Agusta.