Umar A Hunkuyi" />

Tinubu Ya Taya Gowon Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

Jagoran Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya taya tsohon shugaban kasar nan Janar Yakubu Gowon, murna a daidai lokacin da yake cika shekaru 85 da haihuwa a ranar Asabar.

Tinubu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a da dare, ya kwatanta Gowon a matsayin dan kasa nagari wanda ya bayar da gudummawa mai yawa a wajen ginin kasa.

Gowon ya yi aiki a matsayin shugaban gwamnatin mulkin soja na kasar nan daga shekarar 1966-1975.

Tinubu ya ce, “Ina taya tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja na kasar nan murna, Janar Yakubu Gowon, a daidai lokacin da yake cika shekaru 85 da haihuwa a Duniya a ranar 19 ga watan Oktoba, 2019.

“Gowon yana bin Nijeriya bashin yi masa godiya a kan kokarin da ya yi na warware rikicin kabilanci da ya taso wanda ya yi barazanar raba kasar nan da kuma ci gaban da yake yi na aikin ginin kasar nan.

Tinubu ya ce, tun daga lokacin da basasan kasar nan ya wuce bai kuma kara kallon abin da ke bayansa ba, bai kuma gajiya ba a kokarin da yake yi na tabbatar da hadin kan kasar nan.

“Janar Gowon ya ci gaba da aikin da yake yi na wanzar da zaman lafiya da hadin kan kasa da shirin sa na, ‘Nigeria Prays’ project.

“Janar din kuma shi ya kafa ginshikin zaman tarayyan kasar nan tare da kirkiro karin Jihohi da kuma sassa a Nijeriya har zuwa Jihohi 12.

“Janar Gowon kuma yana daya daga cikin shugabannin da suka yi aiki wajen ganin an kafa kungiyar renon Ingila a Afrika ta yamma.

“Ina rokon Allah Ya kara masa tsawon shekaru, da ingantacciyar lafiya domin ya ci gaba da bayar da na shi gudummawar a wajen ginin wannan kasar da kuma kasancewar sa abin koyi ga matasanmu masu tasowa.

Exit mobile version