Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Tinubu Ya Yi Wa Gwamnan Nasarawa Ta’aziyyar Kisan Shekwo

by Muhammad
December 10, 2020
in RIGAR 'YANCI
1 min read
Shekwo
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Umar A Hunkuyi,

Kisan da aka yi wa shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa, Mista Phillip Shekwo, na rashin imani ne, babban jagoran jam’iyyar na kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya kwatanta hakan a ranar Talata.

Tinubu ya yi wa Gwamna Abdullahi Sule da kuma jam’iyyar APC a Jihar ta Nasarawa ta’aziyya a kan kisan shugaban.

An dai sace Shekwo ne daga gidansa wanda daga bisani aka tsinto gawarsa a cikin wani daji a ranar 22 ga watan Nuwamba.

A cikin wata wasikar da ya aike wa Gwamnan, Tinubu yana cewa: “Tare da wannan wasikar ne nake aiko maka da sakon ta’aziyyata a bisa kisan shugaban jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa,  Mista Phillip Shekwo.

“Kisan da aka yi wa Shekwo na rashin imani ne, wanda sam bai cancanta a ce ya mutu ta wannan hanyar ba. Kai sam ma babu wani day a kamata a ce ya mutu ta irin wannan mummunar hanyar.

“Ina mai yi maka ta’aziyya, da gwamnatin Jihar Nasarawa. Ina mai fatan ganin jami’an tsaro sun kai ga zakulo gaskiyan lamarin da zai kai ga kama wadanda suka aikata wannan mummunan laifin.

“Hakanan ina mai mika tra’aziyyata ga iyalan mamacin da kuma tsohon Gwamnan Jihar ta Nasarawa, Alhaji Tanko Al-Makura, wanda ya gabata a kwanan nan gami da daukacin magoya bayan jam’iyyar ta APC a Jihar ta Nasarawa.

“Ina fatan Allah ya ba su hakurin jure wa rashin musamman, ina rokon Allah ya bai wa matarsa da ‘ya’yansa hakurin jure wa wannan rashin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Mutane Miliyan Takwas Ke Mutuwa Sanadiyyar Shan Taba Sigari Duk Shekara

Next Post

An Daure Magini Shekaru 10 Kan Fyade

RelatedPosts

Fyade Fashi

“Na Yi Wa Mata 50 Fyade, Na Yi Wa Gida 100 Fashi”

by Muhammad
22 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Hukumar Sadarwar Tsaro ta Jihar Ondo,...

Duka

Ana Zargin Jami’an DSS Da Lakada Wa Dan Sanda Duka Har Lahira

by Muhammad
22 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Wani jami’in ‘yan sanda da ke...

Makami

An Kama Uba Da ’Ya’yansa Da Laifin Fashi Da Makami A Katsina

by Muhammad
22 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Wani uba da ‘ya’yansa maza biyu...

Next Post
Zargin fyade

An Daure Magini Shekaru 10 Kan Fyade

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version