Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sauye-sauye da kuma shirin samar da kudi da nufin bunkasa fannin aikin noma.
Kazalika, sauye-sauyen; sun hada da zuba Naira tiriliyan 1.5 a Bankin Manoma da kuma samar da rancen kudin noma ga kananan da suka kai Naira 250.
- Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya
- Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle
Babban Ministan Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya sanar da hakan ne a taro karo na 47 na Majalisar Bunkasa Aikin Gona da Samar da Wadattacen Abinci (NCAFS), wanda ta shirya a Kaduna.
Kyari ya ce, tura kudaden zai kasance matakai na saita samar kudade ga fannin aikin noma da kuma samar da wadataccen abinci a kasar.
A cewarsa, Shugaba Bola hmed Tinubu shugaba ne, mai samar da sauyi, kuma yana da yakinin dole ne manoman kasar su koma yin noma da kayan noma na zamani, maimakon dogaro kan kayan aikin noma na gargajiya.
Ministan ya bayyana cewa, daukin da gwamnatin tarayya ta samar a karkashin ajandarta, ya hada da samar da kayan aikin noma na zamani, wanda kuma ya yi da muradun Nijeriya na 2050 na magance asarar da monoma ke yi, bayan sun yi girbi tare da kuma shirin kasa na aikin noma na tsakanin 2021 zuwa 2025 na yin, wato NDP da kuma tsarin yin amfani da kayan zamani, wato NATIP.
Kyari ya kara da cewa, aikin bunkasa fannin aikin noma na kasa, wato NAGS-AP, wanda Bankin Bunkasa Aikin Noma a Afirka, ya kara fadada a daukacin fadin kasar nan.
Ministan ya ci gaba da cewa, noman alkama daga kakar noma ta 2023 zuwa ta 2024, ya karu a jihohi sha biyar, inda kuma nomanta, suka kara karuwa a Jihohin Filato da Taraba da kuma Kuros Ribas.
“Yin amfani da fasahar ta zamani a fannin noman, ya sanya kasar wajen koarin samar da wadataccen abinci da ake bukata a kasar,” in ji Kyrai.
Ministan ya bayyana cewa, domin maganace asarar da manoman kasar ke yi bayan sun girbe amfanin gona da suka kai kimanin dala biliyan 10 a duk shekara, ta kaddamar da wani shiri na kasa mai suna NiPHaST, bisa hadaka da AGRA.
A cewarsa, a karkashin shirin, an tsara za a samar da dauki da ya kai kashi 85, wanda akasari kanannan manoma ne za su amfana ta hayar taimaka musu da kayan aikin noma na zamani da adana amafanin gona da suka jima, wanda za a sayar masu da kayan cikin rahusa.
Kyari ya kara da cewa, Bunkasa Aikin Gona, ya yi hadaka da ‘Heifer Nigeria’, domin wanzar da ajandar shirin samar kayan aikin noma na kasa (RHNAMP), wanda a karkashin shirin za a samar da taraktocin noma da kuma yadda za a kula da su tare da bayar da horo a shiyyoyin koyar da aikin noma da kayan noma na zamani.
Ya kara da cewa, shi ma asusun da ke tallafa wa bunkasa aikin noma na kasa (NADF), ya kuma samar da gudanar da aikin kara fadada zuba hannun jari, musamman domin habaka aikin noma da samun wadatacciyar riba.
Shi ma a nasa jawabin, Karamin Minista a Ma’aikatar Samar da Wadataccen Abinci, Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana cewa; an samar da dabarun magance sauyin yanayi ga fannin aikin noma a kasar.
Abdullahi, ya kuma zayyano wasu shirye-shiye na noman rani a kasar da suka karade hektar noma guda 500,000, wanda yake karkashin shirin Uwargidan Shugaban Kasa Oluremi Tinubu, na yin gangamin samar da ingantacciyar kasar yin noma, wanda kuma aka tsara shirin, bisa samar da kudade, domin habaka fannin aikin noma.
Ya yi nuni da cewa, wannan dabarun za su taimaka wajen rage shigo da kayan abinci cikin kasar nan da kuma kara karfafa kwarin gwiwar kasar duba da cewa, ita ce kan gaba wajen samar da amfanin gona ga Afirka ta Yamma.
“Manufar tamu ita ce, babu wani dan Nijeriya da zai sake yin barci, ba tare da ya samu abincin da zai ci ba,” in ji Abdullahi.
A jawabinsa tun da farko, Babban Sakatare a Ma’aikatar Samar da Wadataccen Abinci, Marcus Ogunbiyi ya bayyana cewa; babbar manufar Majalisar Bunkasa Aikin Gona da Samar da Wadattacen Abinci (NCAFS) shi ne, ganin ana hada karfi da karfe, wajen samar da wadataccen abinci a kasar.
“Daukacinmu, an kira mu ne domin samar da kyakkyawan tsari na samar wa da ‘yan kasar nan wadataccen abinci,” cewar Marcus.
Mayan jami’an Gwamnati daga matakin tarayya da na jihohi da sauran abokan hadaka, sun halarci taron majalisar karo na 47, inda suka tattauna kan yadda za a samar da wadataccen abinci a fadin kasar baki-daya.












