A yau Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu zai rattaba hannu kan wasu dokoki hudu na sake fasalin haraji da zai sauya tsarin tattara kudin shiga a Nijeriya.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar, idan sabbin dokokin harajin suka fara aiki, ana sa ran za su kawo sauyi sosai kan yadda ake tafiyar da harkokin haraji a kasar, wanda hakan zai haifar da karuwar kudaden shiga, da kyautata yanayin kasuwanci, da habaka zuba jari na gida da waje.
A yayin rattaba hannun mai cike da tarihi da shugaba Tinubu zai yi kan kudirin a fadar shugaban kasa, Abuja, ana sa ran, shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kudi, da takwaransa na majalisar wakilai duk za su hallara.