Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Tipa ta Murkushe Dan Achaba A Jihar Ogun

Published

on

A ranar Litinin ne wata tifa ta murkushe wani dan acaba inda nan take ya mutu, a wani hadarin mota wanda ya hada da tifofi biyu da kuma karamar mota kiran Mercedes Benz a Ifo kan babban titin Legas-Abeokuta.
Kakakin rundunar ‘yan sanda Mista Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da faruwar lamarin lokacin ta yake zantawa ga manema labarai. Akinbiyi ya ce, ita dai tifan ba ta da lamba yayin da ita kuma karamar motar mai kiran Mercedes Benz take da lamba kamar haka EG 283 KJA, dukkan su dai hadarin ya rutsa da su a ranar Lahadi da dare inda suka kauce hanya.
Kakakin ya kara da cewa direban tifan yana cikin tafiya ne a ranar Litinin da sassafe, sai motar da kwace masa inda ya murkushe dan acaba mai lambar mashin kamar haka FKJ 8880 KB tare da wadansu mashina biyu wanda aka ijiye a gefe, inda a nan take dan acafan ya mutu.
“Hadarin dai ya faru ne da misalin karfe 5 na safe a layin tsuhuwan banki dake Ifo cikin Abeokuta,” inji shi.
Ya ce, a hanzu haka dai gawar dan acaban an ijiye ta a babban asibitin Ifo. Akinbiyi ya ci gaba da cewa direban tifar da sauran motocin da kuma mashin din da lamarin ya rutsa da su duk suna ofishin rundunar ‘yan sanda na yankin Ifo.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: