Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Tipa Ta Murkushe Dan Achaba A Legas

Published

on

A ranar Litinin ne wata tipa ta murkushe wani dan acaba tare da fasinjansa inda nan take suka mutu a babban titin Legas zuwa Ibadan. Jami’in hulda da jama’a mai kula da hanya Mista Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da faruwar lamarin lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Abeokuta, inda ya ce lamarin ya faru ne kusa da gidan man Connoil dake kan babbata titi. Akinbiyi ya kara da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6.20 na yamma sakamakon mummunan gudun da direban tifan yake yi inda har ta kwace masa, lambar tifan dai shi ne JJJ 472 DP. “Tifan dai ta bugi babur din acaban inda nan take ya mutu tare da fasinjansa,”inji shi.

Akinbiyi ya ci gaba da cewa direban tifan ya tsira, amma wadanda suka matu an garzaya da gawarwakin zuwa asibitin koyarwa na jami’an Olabisi Onabanjo.

“Zan yi amfani da wannan dama domin in jawo hankulan direbobi musamman direbobin tifa da su daina mummunan gudu a kan hanya, su tuna ba su kadai suke amfani da wannan hanyar ba, akwai mutane da dama wadanda suke amfani da wannan hanya,”inji sh

A dai dai lokacin da labaran yadda ake kutsawa cikin asusun mutane a kafafen sadarwa na zamani, akwai tsananin bukatar mutum ya kare mahimman bayanansa daga masu kutse da satar bayanan dake taskace a cikin na’urorinmu na zamani, barayin bayanai a kafafen sadarwa na intanet na haifar da barazana matukar gaske.

Domin kare bayanai daga barayin bayanai kana da bukatar wasu manhajoji da na’urori da zasu taimaka wajen kare muhimman bayanan daka taskace. Zamu kawo muku wasu da zasu taimaka wajen kare tattaunawa da sa ido a kan muhimman bayananka.

  1. Manhajar “Encrypted messenger”

Babu wanda ke son a rinka jin tattaunawar da yake yi da abokanansa ko abokan kasuwancinsa, domin kaucewa haka a kwai bukatar mutum ya samu wannan manhajar tana aiki a wayoyin Android da iOS, wannan mahanjar na jirkita maganganun da ake yi ta yadda ko mutum ya saurari maganan ba zai iya  gane abin da ake nufi ba kuma ba zai iya karantawa ba. wannan mahnajar na iya sarrafa bayanan dake fitowa ta hanyar “boice calls” da “bideo calls” da “group chats” da kuma sakonnin “GIFs” da na “emojis”. Ana iya sarrafa wannan manhajar ta yadda za a iya goge bayanan da aka gudanar a na’uran wanda aka yi tattaunawar da su ana kiran wannan tsarin “Snapchat-style”.

Ana iya samun wannan tsarin a “Facebook” da “IM serbice” da kuma “WhatsApp” suma ana iya samun su a cikin wayan Android dana iOS duk gaba daya suna amfani da Signal ne. An lura mutane da yawa sun fi amfani da WhatsApp wajen tattaunawa amma bai kai tsarin Signal kariyar bayanan mai amfani dasu ba saboda tsarin Whatsapp ana da hanyoyin tsakuro bayanan masu amfani dasu.

  1. Kamara mai sunsuno motsi

Ba dukkanin bayanan kake ajiyewa a cikin intanet ba, na’urori irinsu kwaputa dana wayoyin hannu na dauke da wasu bayanan daka taskace a cikin gidanka amma a kwai wasu na’urorin da zasu iya kara kare bayanan da ka ajiye daga kutsen masu kutse. Domin gano barawo ko mai kokarin bude “fridge” ba tare da izini ba ko kuma domin sa ido akan dabbobi, kana iya amfani da na’urar “Motion-sensitibe camera”. Wannan na’uran na aiki na tsawon awa 24 a kwanaki 7 na mako, zai rika baka bayanan abin dake faruwa kai tsaye za kuma ka iya ganin sakonin ta wayar hanunka, mun zabar maka guda biyu da zasu fi taimaka maka. A kwai wanda ake amfani da shi a cikin daki kawai mai suna “Nest Cam IK” kudinsa Dala 300 ne, yana haduwa da wayar ka, zai sanar da kai ta hanyar yin kara duk lokacin da ya fahinci wani motsin da bai dace ba zai kuma iya banbance tsakanin motsin mutum da na itace. Ana shiga tsarin ne a kan kudi Dala 10 a duk wata ko Dala 100 a duk shekara zai kuma iya ajiye bayanan zirga-zirgan tsawon kwana 10, za a kuma a iya tsara yadda zai iya gane fuskokin ‘yanuwa da abokai ta yadda ba zai yi karar sanar da kai ba.

Za kuma ka iya amfani da kamaran nan mai suna “Netgear Arlo” ana sayar da guda 2 a kan kudi Dala 217, ana iya amfani dasu a ciki da wajen gida domin da batir a ke sarrafa su. Kamar “Nest Cam” ita ma “Arlo’s on-board” na aika sako na kara dana e-mail in ta lura da wani motsin da bata gane ba, ta haka zaka san abin dake faruwa a lokacin da baka gida.

  1. Manhajar BPN

Manhajar BPN kamar na IPBanish duk suna kare bayanai ne daga wanda ba a son ya yi amfani da su. Wannan tsarin na kare tataunawar da ka yi, amma sauran bayanan da ka ke aikawa daga wayar ka fa? A tsarin manhajar “Birtual Pribate Network” dukkan bayanan da ke fitowa ne ake karewa ta haka dukkan bayanan dake fitowa daga wayarka suna samun kariya, ta wannan tsarin yana da wahala kanfanonin sadarwa da hukumonin gwamnati da sauran mutane su iya satar bayanan mu’amalarka a kafafen sadarwa. Manhajar BPN na kyauta baya sauri kamar wanda aka shiga ta tsarin da kudi amma ba haka abin yake a tsarin Opera BPN wadda ke amfani a wayoyin Android da iOS. Yana kuma da saukin sarrafawa, bayan kare tataunawarka, manhajar na kuma hana mutane su gane ainihin in da kake ta hanyar batar da sawunka a duniyar intanet.

Jama’a sun fi nuna sha’awarsu na amfani da manhajar guda biyu saboda aminci da iya aikinsu. Na farko shi ne EdpressBPN wanda wayoyin Android da na iOS na saurin amfani dasu kudadensu ya fara ne daga Dala 8 zuwa Dala 13 a kowanne wata ya kuma danganta da na wata nawa mutum ya siya da kuma dadewar da mutum ya yi wajen amfani da tsarin da kuma yawan watannin da ka nemi amfani da tsarin. Na biyun shi ne IPBanish, shi ma wayoyin Android dana iOS na sarrafa su ba tare da wani wahala ba, ana kuma samu a kan kudi Dala 6.50 da kuma Dala 10 a kowanne wata, shi ma ya danganta da tsawon tsarin da ka shiga, dukkansu ana satarwa tare da kayan sarrafa su wanda zai taimaka wajen kare wayar ka daga kutse, su na kuma bayar da wata daya kyuta domin yin gwaji saboda mutum ya gwada ya ga ingancin na’uran kafin ya fada.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: