Tipa Ta Murkushe Karen Mota A Ogun

A ranar Titinin ne wani direban tifa wanda har yanzu ba a san shi ba, ya murkushe Karen mota a kan doguwar gada da ke babbar yanhar Legas zuwa Ibadan cikin Jihar Ogun. Majiyarmu ta labarta mana cewa, tirela mai lamba DK 252 SMK, ta samu matsala ne a inji da misalin karfe bakwai na safe a kan gadar, yayin da direban tirelan tare da karen motar suka shiga karkashin tirelan suna dubawa, lokacin ne tifan ta murkushe su.
An bayyana cewa, an take Karen motar ya mutu, yayin da direban ya samu mummunar rauni, inda jami’an hukumar kula da hadararruka suka garzaya da shi zuwa asibitin ‘Dibine Touch Hospital’ da ke Ibafo.
Wani wanda lamarin ya auku a gaban idanunsa mai suna Friday, ya bayyana cewa, lokacin da lamarin ya auku nan take direban tifan lamba kamar haka DGB 216 DA, ya mika kansa ga ofishin ‘yan sanda da ke Wawa. Ya ce, “Shi da kansa direban tifa ya mika kansa ga ofishin ‘yan sanda da ke Wawa. Tirelansu ta samu matsala inda direban tare da Karen motar suka shiga karkashin tirelan suna gyara lokacin da kuma tifan ta murkushe su. “Nan take Karen motar ya mutu, amma shi direban jami’an hukumar da ke kula da hadararruka sun garzaya da shi asibiti domin ya samu mummunar rauni.”
Lokacin da aka tuntubi mataimakin kwamantar hukumar FRSC, Olalekan Morakinyo, ya tabbatar da mutuwar Karen motar nan take, yayin da aka garzaya da direban zuwa asibiti. Ya bayyana cewa, lamarin ya auku ne sakamakon rashin saka alama da direban motar tare da Karen motar suka ki, na nuna wa motaci cewa akwai motar da ta lalace a hanya.
Ya ce, “Hatsadin ya auku ne da misalin karfe 7.20 na safe, mutum daya ya mutu, yayin da mutum daya ya samu mummunar rauni. An share hanya, yayin da aka kai wanda ya samu rauni asibitin ‘Dibine Touch Hospital’ da ke Ibafo.
“Motarsu ta lalace akan hanya inda direba tare da Karen motar suke kokarin gyarawa, amma ba su saka alama ba kafin su fara gyaran, inda tafa ta zo a guje sannan ta murkushe su. Direban tifan ya yi tunanin tirelan tana tafiya ne. “Amma akwai rashin lura, idan da direban tirelan tare da Karen motarsa sun saka alama na nisan mita daya da hatsarin bai auku ba.”

Exit mobile version