Yusuf Shuaibu" />

Tirela Ta Murkushe Wata Ma’aikaciyar Hukumar Kula Da Hanya Ta Jihar Legas

Tirela ta murkushe wata ma’aikaciyar hukumar kula da hanya ta Jihar Legasa mai suna Misis Folashade Arogundade, ‘yan shekara 33, har lahira a ranar Asabar. An bayyana cewa, ma’aikaciyar ta na gudanar da aiki ne a yankin Apapa lokacin da tirelan ta murkushe ta a kan hanya. Arogundade ta na kula da cin kosan baban hawa a yankin lokacin da tirelan ta kwace wa direban sannan ta murkushe ta. An bayyana cewa, lamarin ya afku ne ranar Asabar da misalin karfe 4.45.
Wani mutum ya bayyana wa majiyarmu cewa, lokacin da direban tirelan ya tabbatar da buge mutum, sai ya gudu. Ya kara da cewa, sauran abokanan aikinta sun garzaya da ita zuwa babban asibitin Apapa, inda a nan ne likita ya tabbatar da mutuwar ta. Ya ce, “Na ga lokacin da tirelan ta murkushe ma’aikacinyar sa’ilin da direban ya ke juyawa da baya. Bayan tirelan ne ya bug eta, inda tayar baya ta murkushe ta.
“Kafin abokan aikinta su san abinda ya ke faruwa, direban ya gudu daga wajen. Wasu daga cikin abokan aikinta ne su ka kai ta asibiti, inda su ka dawo daga baya su ka bayyana mana cewa ta mutu kafin a isa da ita asibiti.”
Kakakin hukumar kula da hanya ta Jihar Legas, Mista Mahmud Hassan, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana cewa, Arogundade ta mutu lokacin da ta ke gudanar da aikinta na kula da ababan hawa a yankin Apapa. A cewarsa, lamarin ya nuna irin halin direban tirelan. Ya kara da cewa, an gurfanar da direban tirelan a ofishin ‘yan sanda, yayin da ana cigaba da gudanar da bincike a kan direban.
Hassan ya ce, marigayya Arogundade ‘yar shekara 33, ta mutu ta bar yarinya mai shekaru biyu, miji, mahaifiya da kuma mahaifiyar mamanta. Ya cigaba da cewa, mijinta ya na aiki a ofishin karamar hukumar jihar. Ya ce, “an kashe ma’aikaciyar ne ranar Asabar da misalin karfe 4.30 na yamma, kusa da ofishin ‘yan sanda da ke Apapa , inda ta ke gudanar da aikinta a cikin yankin Apapa.
“Tirela ta bug eta lokacin da ta ke gudanar da aikinta. Tirelan ta fara bugun ta ne, yayin da ta fadi inda tayar baya ta murkushe ta. “Nan ta ke abokanan aikinta su ka garzaya da ita zuwa babbar asibitin Apapa, inda a nan ne litika ta ke bakin aiki ya tabbatar da murtuwar ta. An ijiye gawarta a dakin ijiye gawarwaki da ke babbar asibitin Lagos Island domin yin gwaji.”
Shugaban hukumar kula da hanyar ta Jihar Legas, Mista Musa Olawale, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayyan. Ya kuma bayyana cewa, an kashe jami’a hukumar guda 30 a cikin watanni uku da kuma watan Mayun wannan shekarar. Olawal ya yi wannan furici ne a tab akin Hassan, inda ya gargadi masu motoci da kuma daukacin al’umma da su daina yin duk wani lamari da zai kai ga rasa rayuwan jami’an da ke kula da hanya. Ya cigaba da cewa, duk wanda ya sake yin wani lamari da zai kai sa asarar wani jami’an hukumar, ba za dai su dauki doka a hannunsu ba, amma za su mika lamarin ga hukumomin da ya dace, wadanda za su dauki matakin da su ka kamata.

Exit mobile version