Abba Ibrahim Wada" />

Toni Kroos Zai Koma Inter Millan

Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan tana zawarcin dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Tony Kroos dan asalin kasar Jamus.
Kungiyar ta Inter Millan tana buga gasar siriya A kuma akwai tazarar maki 14 tsakaninta da wadda take mataki na daya wato Juventus sannan kuma bata samu damar kaiwa mataki na gaba ba a zagayen kofin zakarun turai da ake bugawa a wannan kakar.
A cewar wani rahoto daga kasar ta Italiya shugabannin kungiyar sun shirya zasu bawa kociyan kungiyar, Luciano Spaletti kudi domin ya kara karfin kungiyar a kakar wasa mai zuwa kuma dan wasa Kroos yana daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar take zawarci domin kara karfi.
Inter Millan dai tana ganin Kroos zai taimakawa dan wasan kungiyar na gaba Mauro Icardi wajen zura kwallo a raga bayan da aka bayyana Kroos a matsayin dan wasan daya iya taimakawa wajen zura kwallo a raga duba da irin bajintar daya nuna a Real Madrid..
Kroos wanda ya buga wasanni sama da 200 a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid yakoma kungiyar ne daga kungiyar Bayern Munchen a shekara ta 2013 inda kuma ya lashe gasar laliga da gasar cin kofin zakarun turai guda uku da gasar Super Cup da kuma kofin duniya amma na kungiyoyi.
Kroos dai mai shekara 28 a duniya baya kokari a wannan kakar wanda hakan yasa ake ganin kungiyar zata iya rabuwa dashi wanda ya lashe gasar cin kofin duniya da kasar Jamus a shekara ta 2006.

Exit mobile version