Tonon Sililin Da ICPC Ta Yi Wa Masu Aringizon Ayyuka A Kasafin 2021

ICPC

Daga Sabo Ahmad,

Hukumar yaki da cin-hanci da karbar rashawa (ICPC) ta bayyana cewa, ta bankado wasu ayyuka da aka maimaita kudinsu guda 257 a kasafin kudin shekara ta 2021, wanda kudadensu suka kai Naira biliyan 20.138.

Sugaban hukumar Farfesa Bolaji Owasanye, ya bayyana haka a wani taro kara wa juna sani, karo na uku da aka yi, kan yadda za a rage cin-hanci da karbar rashawa a wajen gudanar da ayyukan gwamnati, wanda ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya shirya tare da hadin gwiwar hukumar ta ICPC.

Kamar yadda ya ce, hukumar ta bankado daya daga cikin shugabannin da ke da hannun a kan wannan aringizo, wanda kuma an samu takardun bogi masu yawa a hannunsa wadanda ke dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, da na ministoci da hukumar daukar ma’aikata ta kasa da kuma wasu manyan masu mukamai a Nijeriya.

Owasanoye, ya ci gaba da cewa, binciken da hukumar ta ICPC ta yi, ta gano ayyuka guda 1,083 a fadin kasar nan ban da jihar Borno da Zamfara wadanda ba a yi su ba, sakamakon matsalar tsaro da ta addabi wadannan jihohi.

Ya ci gaba da cewa, yanzu haka ana nan ana binciken wasu ‘yankwangila 67, wadanda aka ce lallai sai sun karasa aikin da aka ba su guda 67 wadanda aka ba su a kan kudi Naira biliyan 310 wadanda tuni wadannan ‘yankwangila suka yi watsi da wadannan ayyuka.

Shugaban hukumar ta ICPC ya ci gaba da cewa, wannan yaki ne da suka daura tsakaninsu da dukkan masu aikata irin wannan zamba, saboda haka za su ci gaba da bin sawunsu, tare da gurfanar da su.

Haka kuma shugaban hukumar ya kara da cewa, ICPC za ta ci gaba da bibiyar dukkan wasu ayyuka da gwamnatin tarayya ta bayar domin ta tabbatar da cewa, an yi wadannan ayyuka kuma an yi su masu inganci.

Don haka ne ma, kamar yadda ya ce, taron na bana aka yi masa take da “Cin-hanci da rashawa da kokarin dakile yaduwarsu: Hanya ma fi inganci ta tabbatar da adalci.”

A karsge, Shugaba hukumar ta ICPC ya ce, dole ne a tabbatar da cewa, ana hukunta dukkan wadanda aka kama da laifin cin-hanci da karbar rashawa, yadda zai zama babban darasi ga sauran al’umma.

Exit mobile version