Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Tonon Sililin Mr. Hampher Jakadan Turai A Musulunci Cigaba daga makon shekaranjiya jiya.

by
3 years ago
in ADABI
4 min read
Tonon Sililin Mr. Hampher Jakadan Turai A Musulunci  BABI NA UKU
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

BABI NA SHIDA

Ina nan a Bagadaza babu jimawa aka aiko mini izinin komawa Burtaniya. Kar kuso kuga yadda na cika da murna.

Nan da nan nayi harama, sannan na shiga bin ayari. Sannu a hankali sai gani a ƙasata.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Aka Fitar Da Sakamakon Gasar Rubutun  Hikaya, Na Diyan Gobir

Ta Hanyar Karance-karance Mutum Yakan Zama Marubuci, In ji Fatima Muktar Gombe

Dana isa Landan, na samu cewa hukumar mu taji daɗin yadda alaka ta kullu tsakanina da Muhammad Najd.

Sun kuma gaskata duk abinda na aike musu.a

Acan na gane cewar Safiyya wadda tayi auren Mut’ah da Muhammad Najd tana aikewa da nata sakon wanda bai taɓa cin karo da nawa ba, sannan kuma ashe akwai ‘yan leken asiri da ake sanyawa su bibiye ni a duk inda nake.

Don jin daɗi, sai Sakataren hukumar mu ya shirya mini zama na musamman da ministan hukumar.

Da haɗuwar mu naga ya cika da murna, yana yabon aikin da nayi tare da nuna matukar kauna a gareni.

Ministan shima yaji daɗin yadda na haɗu da Muhammad Najd. Yace mini “ai wannan shine makamin da muka daɗe muna nema”

Na cewa minista “amma kuma ina tsoron zuwa yanzu ya sauka daga kan turbar dana ɗora shi bayan rabuwar mu”

Minista yace “ka daina damuwa, ko kaɗan bai sauka ba”.

Yace mini “akwai ‘yan leken asiri da suka haɗu dashi a Isfahan, har kuma ya tabbatar musu da cewa yana nan kan wannan akida tasa”.

Sai na tambayi kaina a zuciya tayaya Muhammad zai rinka faɗawa mutane irin wannan sirri haka? Amma ban faɗa ga minista yaji ba.

Daga baya dana sake haɗuwa da Muhammad Najd, sai yake labarta mini cewar wani mai suna Abdulkarim yaje gareshi a Isfahan har kuma yace masa shi ɗan uwa nane ya kuma bashi labari na.

Muhammad ɗin ya faɗa mini cewar tare da Safiyya suka isa Isfahan bayan sun sake kulla wata yarjejeniyar auren Mut’ah na watanni biyu.

Shi kuwa Abdulkarim da yace masa ɗan uwana ne ya rakashi Shiraz, acan ya sake nema masa wata mace da tafi Safiyya kyau yayi auren Mut’ah da ita. Sunan ta Asiya.

Sai daga baya na gane cewar wancan Abdulkarim ɗin jakadan kiristanci ne da yake yiwa hukumar mu aiki a ɓoye. Ita kuma Asiya bayahudiya ce dake rayuwa a Shiraz, ita ma kuma jakadiyar hukumar muce.

Mu huɗun nan ne mukayi silar kawar da Muhammad Najd daga turbar da yake kai a farko zuwa wadda muke so.

A lokacin dana kammala bada rahoton tafiya ta ga hukumar mu, sai suka bani hutun kwanaki goma naje na huta kuma naga iyali na.

Daga nan na tafi gida, nayi rayuwa cikin farin ciki dani da matata da kuma ɗana.

Na samu cewar yarona har ya soma tafiya, yana kuma iya faɗar wasu kalmomi.

Gashi yayi matukar kamanceceniya dani.

A cikin lokacin hutuna na ziyarci gwaggona ta wajen mahaifi, amma sai na samu ta rasu bayan tafiya ta. Hakan kuwa yayi mini ciwo.

Sai dai waɗannan kwanaki goma sunyi matukar saurin karewa a gareni. Ina cikin walwala da jindaɗi. Ban lura ba sai gani nayi lokacin har ya cika.

Da ranar komawa ta bakin aiki tayi, sai na tafi ga hukumar tamu, na samu Sakataren hukumar na gaisheshi, nace gani na dawo bakin aiki.

Sakataren yayi musabaha dani, ya jinjina hannuna cikin girmamawa.

Yace dani “akwai wasu sirrika da zan sanar dakai bisa umarnin kwamitin hukumar mu dake lura da larduna da kuma babban minista”.

Yace “nan gaba zaka amfanu da sirrikan sosai, kuma kayi sani sai amintattu kawai ake faɗawa irin waɗannan sirrika”.

Yana rike da hannuna yaja ni izuwa wani zauren tsaro dake cikin ginin hukumar.

Anan na haɗu da wani abu da yaja hankali na.

Mutane goma na gani a zaune bisa kujeru, suna zagaye faffaɗan teburi a tsakiyar su.

Mutum na farko yayi shigar mazauna daular Ottoman ne.

Mutum na biyu yayi shiga kamar ta wani babban malami a Istanbul.

Mutum na uku yayi shiga irinta malaman shia na Iran.

Mutum na huɗu yayi shiga irinta askarawan masarautar Iran.

Mutum na biyar kuwa yayi shiga irin ta manyan malaman shi’a na Najaf.

Sai kuma mutane biyar a kusa dasu a matsayin aSakatarori ga kowannen su.

Akawun hukumar mu yace mini “waɗannan mutane da kake gani, sune ke wakiltar al’ummomin musulmai dake daulolinsu. Kuma mun shirya samar dasu ne domin su rinka yi mana tunani da faɗa mana abinda zai yiwu da wanda ba zai yiwu ba acikin musulunci.

Haka kuma muna danka duk labarun da muka samu daga Istanbul, Tehran da Najaf zuwa garesu domin tabbatarwa da bada fatawa akai. Muna da yakinin duk abinda zasu faɗa zai kusa ko dai-dai da wanda za’a faɗa a inda suke wakilta.

Kuma idan kanaso, kana iya tambayarsu don tabbatarwa tunda kaje ka haɗu da malamai a Istambul da Najaf.”.

Koda naji haka sai na matsa kusa da wani daga cikinsu mai sanye da kaya irin na malumman Najaf, nace “Ya mallam, shin zai yiwu garemu samun umarnin yiwa gwamnatin Ottoman bore tunda gwamnati ce ta mabiya sunni kuma tason zuciya ce?”

Sai ya kada baki yace “sam baya halatta mu yaki gwamnati don tana bin tafarkin sunni tunda duk musulmi ɗan uwan musulmi ne. Zamu yi yaki da ita ne kaɗai idan suka shiga kisan musulmi bisa hujjar umarni da kyakkyawa da hani da mumnuna a garemu. Kuma da zarar kisan nasu ya tsaya, tilas yakin namu ma ya tsaya.”

Nace masa “naji wannan, amma menene ra’ayin ka akan kyamatar yahudu da nasara?”

Sai yace “eh, su ababen kyamatarwa ne, wannan kyama kuwa ta raddi ce kamar yadda suma suke kyamatar mu”.

Duk tambayoyin da nayi masa ya bani amsoshi mafi kusa da irin amsoshin dana samu daga malumman shia a tsawon tafiya ta.

Daga shi sai Sakataren mu yace na matsa ga ɗaya malamin mai sanye da tufafi kwatankwacin na malumman sunni mazauna Istambul nayi tambayoyin gwaji gareshi.

Na matsa ga malamin, sannan na shiga yi masa tambayoyi.

 

Cigaba a mako na gobe in sha Allah.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Wasu Muhimman Kalmomi Game Da Tattalin Arzikin Sin A 2019

Next Post

Ka San Jikinka: Jini

Labarai Masu Nasaba

Rubutun

Yadda Aka Fitar Da Sakamakon Gasar Rubutun  Hikaya, Na Diyan Gobir

by Mukhtar Yakubu
2 months ago
0

...

Marubuci

Ta Hanyar Karance-karance Mutum Yakan Zama Marubuci, In ji Fatima Muktar Gombe

by
2 months ago
0

...

Muluuk

Labarin Asadulmuluuk (17)

by
3 months ago
0

...

Muluuk

Labarin Asadulmuluuk (15)

by
4 months ago
0

...

Next Post
Ka San Jikinka: Jini

Ka San Jikinka: Jini

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: