Abba Ibrahim Wada" />

Torrerira Na Son Barin Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta bayyana cewa dan wasanta na tsakiya, Lucas Torrerira ba na siyarwa bane bayan da suka samu labarin cewa kungiyar kwallon kafa ta AC Milan tana zawarcin dan wasan tsakiyar.

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan dai tana kokarin daukar Marco Giampaolo a matsayin sabon kociyan kungiyar kuma tuni mai koyarwar na Sampadoria ya bayyana Lucas Torreria a matsayin dan wasan da zai fara siya idan ya koma AC Milan din.

Dan wasa Torreira ya koma Arsenal akan kudi fam miliyan 26 inda kuma ya buga wasannin firimiya 34 a kakar wasan data gabata sai dai ya bayyana cewa ba ya jin dadin zaman kasar Ingila inda aka bayyana cewa ya fi son komawa kasar Italiya da buga wasa.

Torrerira, wanda kociyan Arsenal ya siyo shi ya bayyana cewa rayuwa a birnin Landan babu dadi kuma yana fatan ganin yabar Arsenal inda ya zura kwallaye biyu sannan ya buga wasanni 16 amma ba wasannin firimiya ba da suka hada da kofin kalubale da Karabao da kuma gasar cin kofin Europa.

Dan wasan dai ya koma kungiyar kwallon kafa ta Sampadoria ne daga kungiyar Pescara a shekara ta 2016 bayan ya koma kasar Italiya tun yana matashin dan wasa domin fara buga wasa kuma yana cikin tawagar ‘yan wasan kasar Uruguay a yanzu da suke buga kofin Copa America.

Ya fara buga wasan farko ne a Arsenal a ranar 12 ga watan Agustan shekarar data gabata a wasan da Arsenal tayi rashin nasara a hannun Manchester City kuma ya taimaka an zura kwallaye biyar inda kuma ya zura kwallonsa ta farko a wasan da suka doke Tottenham a watan Nuwamban shekarar data gabata a wasan da suka samu nasara daci 4-2.

Exit mobile version