Connect with us

WASANNI

Tottenham Ba Za Su Iya Lashe Firimiya Ba, Cewar Henry

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Thierry Henry, ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham babbar kungiya ce wadda ta yi kokari a ‘yan shekarun nan amma kuma ba su da yawan ‘yan wasan da zasu jure wasannin gasar firimiya har karshe suna samun nasara a kowanne wasa.

Tottenham dai tasamu nasara a duka wasanninta uku data buga na farko a gasar firimiya sai dai kungiyar tasha kasha a wasanni uku data buga a jere kafin ta samu nasarar doke Brighton a satin daya gabata sannan  bata siyi dan wasa ko daya ba a kasuwar siyan ‘yan wasan da aka rufe a watan Agustan daya wuce hakan yasa  Henry yake ganin abune mai wahala kungiyar ta iya lashe firimiya da ‘yan wasan da take da su a yanzu.

Sai dai Henry ya ce kungiyar tayi kokari wajen hana ‘yan wasanta tafiya kamar Erikson da Harry Kane inda ya ce sun yi babban aiki na hana wasu daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar tafiya duk da cewa manyan kungiyoyi irinsu Real Madrid da Barcelona sun nemi ‘yan wasan.

“Wannan ce shekarar da yakamata Tottenham ta samu nasarar lashe firimiya saboda suna da ‘yan wasa kuma suna da dan wasa mai girma kamar Harry Kane sannan ga Delle Ali da babban mai tsaron raga waro Hugo Lloris da kuma Erickson”  in ji Paul Merson.

Ya ci gaba da cewa “Dan wasa Lucas Moura  wanda kungiyar ta siya a watan Janairun da ya gabata daga kungiyar PSG yana taimakawa kungiyar sosai kuma ya zama kamar sabon dan wasa a kungiyar saboda a wannan kakar ya shiga cikin kungiyar”

A karshe ya ce yana ganin yakamata kungiyar a wannan kakar ta samu nasarar lashe kofi guda daya a kasar Ingila idan har suna son su cigaba da rike ‘yan wasansu wadanda manyan kungiyoyi suke nema saboda ya ce cin kofi shine yake sa dan wasa ya zauna a kungiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: