Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Machael Owen, ya bayyana cewa kungiyar Tottenham wadda Jose Mourinho yake koyarwa ba zata iya lashe gasar firimiya ba saboda karancin kwararrun ‘yan wasan da zasu jure buga wasanni da yawa.
Tottenham ta yi nasara a kan Arsenal da ci 2-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi bayan dan wasa Heung-min Son ya fara cin kwallo a minti na 13 da fara wasa kafin daga baya ya taimakawa Harry Kane ya kara ta biyu daf da za su je hutun rabin lokaci.
Kawo yanzu kaftin din kungiyar Harry Kane ya ci Arsenal kwallo 11 kenan a dukkan fafatawa da suka yi, kuma shi ne kan gaba a Tottenham wajen cin Arsenal a tarihi amma kafin nan dan wasa Emmanuel Adebayor da kuma Bobby Smith ne kan gaba a Tottenham wajen zura kwallo a ragar Arsenal.
Wasa na bakwai kenan da kungiyoyin suka kara a gasar Premier League a gidan Tottenham wadda ta ci wasa biyar da canjaras biyu kawo yanzu kuma fafatawa ta 11 da Mourinho ya yi a gida da Arsenal ba ta yi nasara a kan kocin ba.
A fafatawar da Arsenal ta yi rashin nasara karo biyu a jere a hannun Tottenham ita ce sau biyu a watan Mayun shekarar 1993 da kuma a Nuwamban shekara ta 2010 sai dai da wannan sakamakon Tottenham ta koma mataki na daya a kan teburin Premier League da maki 24, bayan buga wasa 11 Arsenal ma karawa 11 ta yi a gasar bana, ta hada maki 13 tana mataki na 15 a kasan teburi.
Ranar Alhamis 10 ga watan Disamba, Arsenal za ta ziyarci Dundalk a wasa na shida-shida a cikin rukuni a gasar Europa League sannan a kuma ranar Tottenham za ta karbi bakuncin Royal Antwerp a dai wasan karshe na cikin rukuni a gasar ta Zakarun Turai.
Wadanda suka yi alkalancin wasan Premier ranar Lahadi::