Connect with us

WASANNI

Tottenham Ta Ce Ba Za Ta Siyarwa Da Barcelona Dan Wasanta Ba

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta gargadi kungiyar kwallon kafa ta Barcelona cewa dan wasanta Christian Erickson dan kasar Denmark ba na siyarwa bane akan kowanne farashi duk da cewa tana nemansa.

Barcelona dai ta ayyana Erickson a matsayin dan wasanda zai maye mata gurbin Andries Iniesta, wanda yabar bugawa kungiyar wasa a kakar wasan data gabata inda yakoma kasar Sin, wato China da buga wasa.

A kwanakin baya dai Eriksen ya taba bayyana cewa abune mai wahala Barcelona tace tanason dan wasa kuma yace baya son zuwa saboda haka bazai iya cewa bazai taba komawa Barcelona ba amma kuma yana farin ciki a kungiyarsa.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta yiwa Eriksen kudi sama da fam miliyan 200, kudin da Barcelona ta karba a hannun PSG akan Neymar kusan shekara daya da rabi.

Sai dai abune mai wahala kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta siyar da dan wasan wanda take ganin batada kamarsa a yanzu kuma itama tana ganin tazama babbar kungiya a halin yanzu saboda tana zuwa gasar cin kofin zakarun turai.

Barcelona dai ta siyi dan wasa Arturo Bidal daga kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen sai dai har yanzu hankalin kungiyar bai kwanta ba a ‘yan wasanta na tsakoya sakamakon duk sun fara tsufa kuma tana bukatar karin ‘yan wasa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: