Abba Ibrahim Wada" />

Tottenham Ta Dauki Sabon Mai Tsaron Raga

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta sake daukar mai tsaron raga Michel Borm domin ya tsare ragarta zuwa karshen kakar bana, bayan da Hugo Lloris ke jinya sakamakon ciwon da yaji makonni biyu da suka gabata.

Dan kasar Netherlands mai shekara 35, ya bar Tottenham a karshen kakar bara, bayan da yarjejeniyarsa ta kare ta kungiyar ku–ma kociyan kungiyar ya bayyana cewa bazasu kara masa sabon kwantiragi ba.

Kyaftin din kungiyar, Hugo Lloris, dan kasar Faransa, ya samu rauni ne a wasan da Tottenham ta yi rashin nasara a hannun Brighton Albion a gasar firimiya daci 3-0, wanda zai yi jinya zuwa Janairun sabuwar shekara ta 2020.

Borm ya fara zuwa Tottenham ne a shekara ta 2014 daga kungiyar kwallon kafa ta Swansea City, ya kuma buga mata wasanni 47 sai dai daga Tottenham din kuma sai ya koma gida da buga wasa.

Mai tsaron ragar zai saka riga mai lamba 13 wadda ya saka a baya, zai kuma tsare raga ranar Asabar a wasan firimiyar da Tottenham za ta yi da Watford wasan da kungiyar tasa take bukatar samun nasara mutuka.

Tottenham na fama da kalubale a kakar bana, bayan da Colchester ta fitar da ita a gasar cin kofin Caraboa a bugun fenariti haka kuma kungiyar ta yi rashin nasara a gasar firimiya a hannun Leicester City da Brighton a bana, sannan Bayern Munich ta doke ta daci 7-2 a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League.

Exit mobile version