Abba Ibrahim Wada" />

Tottenham Tana Cikin Gagarumar Matsala, Cewar Mourinho

Mourinho

LONDON, ENGLAND - JANUARY 22: Jose Mourinho, Head Coach of Tottenham Hotspur talks to his players in the tunnel at half time during the Premier League match between Tottenham Hotspur and Norwich City at Tottenham Hotspur Stadium on January 22, 2020 in London, United Kingdom. (Photo by Tottenham Hotspur FC/Tottenham Hotspur FC via Getty Images)

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Jose Mourinho ya bayyana cewa kungiyarsa tana cikin gagarumar matsala bayan da suka sha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Brighton Hobe Albion da ci daya mai ban haushi.

Tottenham dai ta buga wasan ne ba tare da dan wasanta na gaba ba, Harry Kane, wanda yaji ciwo a wasan da suka fafata a satin daya gabata da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wasan da sukayi rashin nasara daci 3-1.
Shima mai hoarr da ‘yan wasan Brighton, Graham Potter ya ce ‘yan wasan sa sun yi bajintar da rabonsu da yi shekaru biyu kenan da suka wuce, bayan da suka doke Totenham da ci daya mai ban haushi, inda suka baiwa kungiyoyi uku da ke kasan teburin gasar Firimiya tazarar maki 7.
dan wasa Leandro Trossard ne ya ci kwallo daya tilo na wasan, bayan mintina 17 da fara wasa kuma haka Brighton masu masaukin bakin suka rike wuta a filin wasansu na Amed, kuma ba su saki ba har sai da suka samu nasararsu ta farko a gida tun watan Yunin bara.
Potter ya shaida wa manema labarai cewa wannan wasa shine ne bajinta mafi armashi da ‘yan wasansa suka yi a karon farko cikin kakanni biyu kuma yana fatan zasu sake dagewa domin dorawa akan wannan nasarar da suka samu.
Kocin Tottenham, Jose Mourinho, wanda tawagarsa ke matsayi na 6 a teburin Firimiyar Ingila ya ce lallai ‘yan wasansa ba su yi farin ciki a  filin wasan ba saboda sun damu ainun da rashin shahararren dan wasansu, Harry Kane da sauran ‘yan wasa.

Exit mobile version