Shi dai shugaban Amurka mai ci, Donald Trump, ba shi da abin yi face janyo magana. Yawancin kalaman da za ka ji ya furta ko gwamnatinsa ta furta, za ka tarar ba su yiwa mutane da yawan gaske dadi ba. Idan kuma sun yiwa wasu dadi, to za ka riska cewa, watakila sun sa`a da wata ka’ida ko kuma ma ita kanta doka bakidaya ko wata yarjejeniyar mutuntaka.
Abu ne da ya ke a bayyane cewa, Nijeriya da Amurka su na da matukar fahimtar juna tun bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama shugaban Nijeriya a babban zaben kasar na shekara ta 2015, wanda ya kawo karshen mulkin jam’iyyar da ta dade tan a jan zarenta a kasa, wato PDP.
A al’adar kas ashen duniya, musamman ita kanta Amurka, su na girmama kasashe abokansu na diflomasiyya, musamman wadanda ke jagorori ne a yankunansu, kamar Nijeriya a Afrika, Saudiyya a Gabas ta Tsakiya, Indiya a yankin Asiya da sauransu, ba tare da la’akari da wacce jam’iyya c eke mulkin Amurka a lokacin ba, wato Republic ko Democrat.
To, amma babban abin takaicin da ya samun Amurka a yanzu shi ne yadda irin wadannan kasashe na kawancenta su ke fuskantar gwasalewa daga gare ta ba tare da la’akari da abinda ka je ya komo ba.
To, ba mu ce sai ta yi aiki da shi ba, amma abin takaicin shi ne, babu dattaku a bayar da irin wannan sanarwa babu gaira babu dalili. Kamata ya yi a ce, Amurka ta nuna halin manyance da mutuntaka ta hanyar kin tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan Nijeriya, domin kasar abokiyarta ce kuma ta na da matukar amfani a siyasar duniya, musamman idan a na son hadin kan Afrika kan wasu manufofi na duniya.
Shugabannin Amurka na baya ba za su bari a aikata irin wannan danyen hukunci ba, saboda hangen nesansu da kuma mutuntakarsu, wanda wannan ya na taimakawa wajen rangwantawa Amurka da manufofinta a kasashe irin Nijeriya da sauransu. Abokin kirki bay a kwance ma ka zani a kasuwa koda kuwa ka yi wani kuskure ne, sai dai kare ka a bainar jama’a, amma ya ja ka daki ya gaya ma ka, don ka gyara a gaba.
To, amma da ya ke shi Trump da manufofinsa tamkar jaba ne, ki tsoma baki a abinci a bar mi ki, bai damu da irin wannan wautar ba, wacce a karshe za ta iya kai Amurka ta baro ta! Kowane tsuntsu kukan gidansu ya ke yi, kuma kowa da ranarsa!!!