Daga Rabiu Ali Indabawa
Bayan nasarar ƙulla yarjejeniya tsakanin ƙasar Amurka Iran, game da makamin Nukiliya, Shugaba Trump na ƙasar Amurka ya ɗauko hanyar gurgunta yarjejeniyar. A makon gobe ne ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai ayyana yarjejeniyar Nukiliyarr da Amurka da wasu manyan ƙasashen duniya suka ƙulla da Iran a zaman gurguwar yarjejeniya, da kiris yake rage shugaban ya ayyana yarjejeniyar a zaman maras tasiri. Shugaba Trump zai faɗa cewa yarjejeniyar da aka ƙulla a shekarar 2015, ba za ta taimaki tsaron Amurka ba.
Matakin zai ƙaddamar da wa’adin kwanaki 60 ga majalisun dokokin Amurka su yanke shawara ko za su sake ƙaƙabawa Iran takunkumin karya tattalin arziƙi,da aka janye bayan da aka cimma yarjejeniyar.
Wakilai ‘yan jam’iyyar Democrat da Republican masu yawa suna adawa da sake ƙaƙabawa Iran takunkumi, wanda yain hakan zai soke yarjejeniyar baki ɗaya.
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi barzanar Iran za ta yi da yarjejeniyar da zarar Amurka ta sake aza mata takunkumi.