Khalid Idris Doya" />

Trump Ya Sa Wa Mexico Sabon Haraji

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasar za ta dora harajin kashi 5% kan duk wasu kayayyakin da ke fitowa daga kasar Mexico har sai zuwa lokacin da bakin haure suka daina tsallaka iyakar Mexico domin shiga Amurka.

Shugaba Trump ya sanar da wannan shiri ne ta hanyar da ya saba aikewa da sako wato kafar twitter, inda yake cewa daga ranar 10 ga watan Yuni mai zuwa, Amurka za ta dora wa Medico karin kashi 5 na kudin fiton kayan da take kai wa kasar, har sai zuwa lokacin da bakin haure suka daina shiga kasar.

Trump ya ce za a ci gaba da kara harajin har sai an tabbatar da cewar an shawo kan matsalar kafin a janye shi.

Karin hasken da fadar shugaban ta yi ya ce daga ranar 1 ga watan Yuli kudin fito zai tashi zuwa kashi 10, kana za a dinga kara kashi 5 kowanne wata har sai ya kai kashi 25 nan da ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

A wasikar da ya rubuta masa bayan wannan sanarwa, shugaban kasar Mexico Andres Lopez Obrador, ya bukaci tattaunawa, inda ya ce ba a bukatar yin fito na fito tsakanin kasashen biyu.

Exit mobile version