Shugaban Amurka, Donald Trump, tare da mataimakinsa JD Vance, sun sake ɗarewa kan mulki bayan rantsuwar kama aiki da aka gudanar a ranar Litinin, bayan wa’adin Joe Biden da Kamala Harris ya cika.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a ɗakin taro na majalisar dokokin Amurka, inda manyan baƙi daga ciki da wajen ƙasar suka halarta.
- Nijeriya Ta Yaba wa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gaza
- Sin Ta Yi Maraba Da Matsayin Da Najeriya Ta Samu Na Zama Abokiyar Huldar Gamayyar BRICS
A jawabinsa bayan rantsuwar, Trump ya bayyana sabbin ƙudirorinsa da zai aiwatar a wannan wa’adi, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta dawo da martabar Amurka a idon duniya, ta tabbatar da tsaro, da kuma haɗa kan jama’ar ƙasar.
Sabbin matakan da ya bayyana sun haɗa da:
- Sanya dokar ta ɓaci a iyakokin kudancin Amurka don daƙile kwararar baƙi da tura dakarun soja.
- Korar duk wani baƙo da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba.
- Zartar da dokar rage farashin makamashi ta hanyar haƙo mai a cikin gida.
- Soke dokokin kare muhalli da wajabta amfani da motoci masu lantarki.
- Ƙirƙirar hukumar tattara haraji daga ƴan ƙasashen waje.
- Amincewa da jinsi biyu kawai a hukumance: Namiji da Mace.
- Dasa tutar Amurka a duniyar Mars.
- Ƙwace iko da mashigin ruwa na Panama Canal da sauya sunayen wasu wuraren tarihi kamar gaɓar ruwan Mexico da tsaunin Denali.
Trump ya yi alfahari da cewa kafin rantsar da shi, an cimma tsagaita wuta a yakin Gabas ta Tsakiya, abin da ya ce zai ƙara tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Sabuwar gwamnatin Trump na shirin aiwatar da sauye-sauyen da suka janyo cece-kuce, inda yake burin ganin Amurka ta zama ƙasa mai fice fiye da kowane lokaci.