Trump Ya Sake Ɗarewa Kan Mulkin Amurka, Sabbin Ƙudirorinsa Sun Bar Baya Da Ƙura
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Trump Ya Sake Ɗarewa Kan Mulkin Amurka, Sabbin Ƙudirorinsa Sun Bar Baya Da Ƙura

bySadiq
9 months ago
Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, tare da mataimakinsa JD Vance, sun sake ɗarewa kan mulki bayan rantsuwar kama aiki da aka gudanar a ranar Litinin, bayan wa’adin Joe Biden da Kamala Harris ya cika.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a ɗakin taro na majalisar dokokin Amurka, inda manyan baƙi daga ciki da wajen ƙasar suka halarta.

  • Nijeriya Ta Yaba wa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gaza
  • Sin Ta Yi Maraba Da Matsayin Da Najeriya Ta Samu Na Zama Abokiyar Huldar Gamayyar BRICS

A jawabinsa bayan rantsuwar, Trump ya bayyana sabbin ƙudirorinsa da zai aiwatar a wannan wa’adi, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta dawo da martabar Amurka a idon duniya, ta tabbatar da tsaro, da kuma haɗa kan jama’ar ƙasar.

Sabbin matakan da ya bayyana sun haɗa da:

  • Sanya dokar ta ɓaci a iyakokin kudancin Amurka don daƙile kwararar baƙi da tura dakarun soja.
  • Korar duk wani baƙo da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba.
  • Zartar da dokar rage farashin makamashi ta hanyar haƙo mai a cikin gida.
  • Soke dokokin kare muhalli da wajabta amfani da motoci masu lantarki.
  • Ƙirƙirar hukumar tattara haraji daga ƴan ƙasashen waje.
  • Amincewa da jinsi biyu kawai a hukumance: Namiji da Mace.
  • Dasa tutar Amurka a duniyar Mars.
  • Ƙwace iko da mashigin ruwa na Panama Canal da sauya sunayen wasu wuraren tarihi kamar gaɓar ruwan Mexico da tsaunin Denali.

Trump ya yi alfahari da cewa kafin rantsar da shi, an cimma tsagaita wuta a yakin Gabas ta Tsakiya, abin da ya ce zai ƙara tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Sabuwar gwamnatin Trump na shirin aiwatar da sauye-sauyen da suka janyo cece-kuce, inda yake burin ganin Amurka ta zama ƙasa mai fice fiye da kowane lokaci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa
Manyan Labarai

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Next Post
Tinubu Ya Dawo Nijeriya Bayan Ziyarar UAE, Zai Mayar Da Hankali Kan Muhalli Da Haɗin Gwiwa

Tinubu Ya Dawo Nijeriya Bayan Ziyarar UAE, Zai Mayar Da Hankali Kan Muhalli Da Haɗin Gwiwa

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version