Yusuf Shuaibu" />

Tsadar Sufuri Ta Kara Tsauwala Farashin Abinci A Yuli– NBS

Abinci

Hukumar Kiddiga ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabi a watan Yulin shekarar 2020, sakamakon dan karen tsadar da harkokin sufuri suka yi.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahotonta na nazarin yadda hada-hadar kayan abinci ta gudana a cikin watan Yulin shekarar 2020.

An dai wallafa wannan rahoto ne a shafin intanet na hukumar a ranar Alhamis. Rahoton bayanan farashin kayayyakin abincin na watan Yulin shekarar 2020, ya nuna cewa, ana samun karin kashi 1.24 a cikin dari a duk wata.

Hukumar ta kara da cewa, farashi tumatir ya karu da kashi 49.34 a watan Yulin shekarar 2020 wanda ake sayar da shi a watan kan Naira 304.01, idan aka kwatanta shi da na watan Yulin shekarar 2020 wanda yake kan Naira 294.46.

Hukumar NBS ta ce har zuwa lokacin wannan kididdagar, farashin shinkafa mai nauyin keji daya ya karu da kashi 37.72, wanda aka samu karin kashi 2.23 a kan yadda ake sayarwa a watan baya, a watan Yuli dai ana sayar da ita a kan Naira 490.44, inda a watan Yunin shekarar 2020 ake sayar da ita kan Naira 479.74.

Rahoton ya bayyana cewa, farashin kilo daya na doya ya karu da kashi 50.10, wanda ake sayar da shi a kan Naira 256.44 a watan Yuli, yayin da aka sayar da shi a kan Naira 250.70 a watan Yunin shekarar 2020.

A cikin rahoton mai taken ‘harkar sufuri ya kara farashin kayayyakin abinci a watan Yulin shekarar 2020’, hukumar kididdigar ta kasa ta bayyana cewa, farashin sufuri ya karu da kashi 7.66, inda ake biyan Naira 247.46 a watan Yulin shekarar 2020, yayin da aka biya Naira 229.49 a cikin watan baya na Yuni.

Hukumar NBS ta ce, “kudaden sufuri sun karu da kashi 7.62 a cikin watan. Jihohin da suka fi samun karin dai sun hada da Zamfara wand aka sami karin Naira 500.40 da Nassarawa wanda aka sami karin Naira 358.20 da kuma Jihar Kuros Ribas wacce ta sami karin Naira 350.00, a bangare daya kuma, jihohin da suke da karancin sufuri ta bas-bas dai sun hada da Bauchi wacce take da karin Naira 145.10 da Ribas da ke da karin Naira 170.00 da kuma Jihar Kebbi wacce ake biyan karin Naira 170.20,” in ji rahoton na NBS.

Exit mobile version