Daga Abubakar Abdullahi, lafia
Daya daga cikin abubuwan da aka fi dubawa ga jagorar gwamnati shi ne, irin dangantaka da ke wanzuwa tsakanin ma’aikata da shugabanni domin hakan na daga abuwan da ke nuna kyawu ko akasin haka na wanda ke gaba a tafiyar da harkokin gwamnati kowace iri ce.
A Jihar Nasarawa dangantaka tsakanin Gwamna Umaru Tanko Al-Makura da ma’aikatan gwamnati tun farkon wa’adin mulkinsa a shekarar 2011, ta fara ne bangarorin biyu na haba-haba da juna saboda wanzuwar kyakyawar dangantaka.
Da hawarsa mulki a shekarar 2011 Gwamna Al-Makura ya mayar da hankali a kan abubuwan da za su inganta jin dadi da walwalar ma’aikata, inda cikin watannin farko da kamun ludayinsa, gwamnan ya aiwatar da tsarin biyan albashi mafi karanci na naira dubu goma sha takwas ga ma’aikata a fadin jihar.
Wannan abin da Gwamna Al-Makura ya aiwatar ya inganta jin dadin ma’aikata da iyalansu lamarin da janyo masa yabon jama’a a ciki da wajen jihar kasancewarsa daya daga cikin jerin gwamnonin da suka aiwatar da tsarin biyan albashi mafi karanci na naira dubu goma sha takwas ga ma’aikata a fadin kasar nan. Ba wai kawai aiwatar da tsarin da Gwamna Al-Makura ya yi ba, gwamnatinsa ta kasance tana biyan albashi a kan kari.
Wannan ya sa ma’aikata suka kasance masu yabon gwamnan ganin yadda ba ya wasa da albashinsu. A wannan yanayin su ma ‘yan kasuwa a jihar sai darawa suke domin duk lokacin da aka yi biyan albashi ga ma’aikata kasuwanni da sauran wuraren cinikayya a jihar sukan koma matattarar ma’aikata inda kowannensu ke sayayyar abin bukata ciki jin dadi da annashuwa sakamakon yanayi da tsarin albashi da suke karba.
Haka dai lamarin ya ci gaba da kasancewa na tsawon fiye da shekaru hudu har ta kai ga ma’aikata da sauran mazauna jihar na yi wa Gwamna Al-Makura kirari da ‘Gwamnan Ma’aikata’ ganin yadda yake ji da su, su ma suna kewansa. Da tafiya ta yi tafiya, bayan Gwamna Al-Makura ya lashe zabe karo na biyu a matsayin gwamnan jihar, sakamakon matsin tattalin arziki da kasa ta shiga wanda ita ma Jihar Nasarawa ba ta tsira ba.
Matsin tattallin arzikin ya shafi jihar matuka gaya domin yawan kason kudade da ke shigowa lalitar gwamnatin jihar ya ragu sosai. Haka ma kudaden da ake samu cikin jihar a matsayin haraji ga gwamnati ba su taka kara sun karya ba idan aka yi la’akari da irin bukatun da jihar ke da su.
Wannan ya sa gwamnati kiran taro tsakaninta da ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyar da za a bi sakamakon karancin kudi a iya yi wa al’umma ayyuka da kuma biya ma’aikata albashinsu ba tare da wata matsala ba.
A yayin taron dai mahalarta sun yi tsokaci daban-daban. A karshe dai gwamnati ta nuna wa ma’aikata cewa an kuskure wajen yin lissafin ainihin adadin abin da ya dace a biya kowane ma’aikaci a matsayin albashi kuma yanayi da ake ciki ba zai bai wa gwamnati damar ci gaba da biyan irin albashin da saba biya ba kafin shiga matsin tattalin arzikin. Gwamnatin ta janyo hankulan ma’aikatan cewa tilas a yi wani abin da ba zai shafi harkokin gwamnati ba kuma ma’aikata ba za su cutu ba game da irin albashi da za su karba idan aka yi sauyin.
A nasa tsokaci, gogaggen tsohon ma’aikacin gwamnatin nan kuma sakataren gwamnatin Jihar Nasarawa na farko wanda ya rike mukamin ministan kwadago a zamanin mulkin Obasanjo Husseini Zanwa Akwanga, ya ce yanayi da ake ciki na matsin tattallin arziki ya nuna karara cewa tilas gwamnati da ma’aikata su rage buri na abin da ake so a yi wa jama’a da kuma biyan ma’aikata albashinsu daga cikin adadi na kudaden da gwamnati ke samu walau daga Gwamnatin Tarraya ko harajin da gwamnatin jihar ke karba daga kamfanoni da daidaikun mutane.
Sai dai da yake jawabi a yayin taron, shugaban kungiyar kwadago a jihar Abdullahi Adeka, bai nuna cewa ma’aikata za su amince da rage musu kudadensu na albashi kai tsaye ba amma ya ce ma’aikata za su yi na’am da duk wani sauyi da ba zai cutar da su ba. ‘Yan makonni bayan taron ne gwamnati ta sake ganawa da shugabanin kungiyar kwadago a gidan gwamnatin jihar da ke Lafia inda dangarorin biyu suka tattauna suka kuma fitar da sabon tsarin albashi ga ma’aikata wanda ya rage yawan albashin ma’aikata, sai dai ma’aikatan kiwon lafiya da na bangaren shari’a ne kawai hakan bai shafa ba.
A lokuta daban-daban da suka yi bayyanai kan bullo da sabon tsarin albashi, Gwamna Al-Makura da wasu manyan jami’an gwamnatinsa sun ce an yi kuskure wajen tsarin albashin tun farko inda a cewarsu, dokar tsarin ya ce kar ma’aikacin gwamnati ko mai rashin matsayinsa a matakin aiki albashinsa ya kasa naira dubu goma sha takwas. Su kuma manyan ma’aikata daga mataki na 7 zuwa na 17 a yi mu su kari kan abin da ake ba su na albashi ta yadda za a samu bambanci da kowane ma’aikaci zai dara.
To amma maimakon haka gwamnatin Jihar Nasarawa a cewar masu bayanin ta ninka albashin dukkanin ma’aikata har sau uku ko ma fiye da hakan. Sun kara da cewa duk da gwamnatin ta fahimci wannan kuskuren kuma kudaden da ke shigowa a wancan lokacin sun isa a rinka biyan ma’aikata har ma a ci gaba da gudanar da ayyuka ga al’ummar jihar, gwamnatin ba ta damu ba ta a hakan ta ci gaba da biyan ma’aikata.
Sun ce tun da an samu ragi na kudaden da ke shigowa jihar akwai bukatar sauyi kan yadda ake biyan albashin ma’aikata. To amma matakin da aka dauka na yin sauyin bai yi wa ma’aikatan dadi ba. Hasali ma kungiyar kwadago a jihar ta ce zaman da ta yi da gwamnati ba matsayar da suka cimma ba kenan. An yi kai gwauro da mari tsakanin gwamnati da ma’aikata domin gwamnati ta sauya matsayinta game da albashin to amma hakan bai samu ba har ta kai ga ma’aikata suka gudanar da zanga-zanga da shiga yaje- yajen aiki.
Yaje-yajen aikin da ya kai ga shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa Ayuba Wabba, ya zo jihar domin sassanta tsakanin ma’aikata da gwamnatin jihar. Sai dai wani abin da a iya cewa ya so ya bata zuwan sassantawa na shugaban kungiyar shi ne, yayin da shugaban kungiyar kwadagon da ‘yan tawagarsa ke zaman jiran tattaunawa da Gwamna Al-Makura a fadar gwamnatin jihar sai wata hatsaniya ta barke a kofar shiga fadar tsakanin ma’aikatan gwamnati da ke zaman jiran shugabanninsu da babban manajan tashar rediyo da talabijin mallakar gwamnatin jihar Yusuf Musa wanda ya zo zai shiga fadar gwamnatin.
A yayin wannan hatsaniya ne ma’aikaci guda ya rasa ransa nan take yayin da wani ma’aikaci guda ya samu rauni sakamakon harbin bindiga daga jami’an tsaron da ke kokarin shiga tsakani inda aka garzaya da shi asibiti daga bisani ya ce ga garinku nan baya ga wadanda suka samu rauni aka yi musu magani suka warke.
Wannan lamari ya so hana zaman sulhun to amma daga bisani bayan da shugabannin kungiyar kwadago suka dubi gawar ma’aikacin da ya fara mutuwa a hatsaniyar da wadanda suka ji rauni, sai aka gudanar da zaman. A yayin zaman ne ma shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba, ya yi Allah-wadai da abin da ya faru sannan ya bukaci a zakulo wadanda ke da hannu a hatsaniyar a kuma hukunta su.
Shi ma da yake magana game da lamarin, Gwamna Al-Makura ya bayyana alhininsa kan abinda ya farun tare da yin ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa ransu cikin lamarin, yana mai cewa za a yi bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru da kuma yin hukunci a kai.
Duk da irin wannan abin da ya faru, bai sa gwamnati komawa da baya kan matakin da ta dauka na sauyin tsarin albashi ba bisa hujjar da ta kafe a kai ta karancin kudi a jihar. Sai dai ana cikin wannan yanayi ne gwamnatin da ma’aikata suka shiga yarjejeniya a tsakaninsu kan duk watan da ya zo idan kudin da ake da shi bai kai a biya albashi ba, to za a ajiye a jira a hada da na watan gaba sannan a biya albashin wata guda maimakon biyan rabi.
Sai dai ba a dauki lokaci ana aiki da yarjejeniyar ba ma’aikata suka sake tada balli cewa akwai kudi da za a rinka biyan su albashi cikakke da gangar gwamnati take musu tana ink biyansu a kan lokaci. Yanayin ya kara zafafa ne inda ma’aikatan suka bukaci a biyasu bashin da suka ce suna bi na albashin wasu watanni sannan sun daina karbar albashi da suka ce rabi ne na abin da ya dace a ba su ko kasa da haka. Ma’aikatan sun kuma bukaci gwamnati baya ga ta rinka biyansu cikakken albashi da basussukansu, ta kuma biya su wasu hakkokinsu da suka hada da karin girma da kudaden alawus-alawus da dai sauransu.
Wannan ya sa a cikin watan Mayu na wannan shekarar bikin ranar ma’aikata da Gwamna Al-Makura ya saba halarta inda yakan yi wa ma’aikata alkawura, ma’aikatan sun ki bada hadin kai game da bikin. Maimakon hakan, ma’aikatan sun taru ne a sakatariyar kungiyar kwadago ta jihar da ke hanyar Makurdi a Lafia sanye da bakaken tufafi inda a jawaban shugabanninsu sun bukaci ko dai gwamnati ta biya musu bukatunsu ko kuma su koma yajin aiki irin na sai baba ta gani.
Sai dai a iya cewa hakan wani matakin da a iya cewa na samar da hanyar kawo karshen yajin aikin ne duk da cewa gwamnati ta ce ba ta san ana yajin aiki ba saboda bangaren da take hulda da shi na shugabannin ma’aikatan ba ya yajin aiki, gwamnatin ta aiwatar da karin girma ga malaman makarantun sakandare sama da dubu shida wadanda su ne suka fi yawa a ma’aikatan da ke yajin aikin. Duk dai hakan bai sa an janye yajin aikin ba duk da kiraye-kirayen da masu ruwa da tsaki ke ta yi ga ma’aikata da gwamnatin a kan su sasanta a janye yajin aikin domin kawar da wahalhalun da hakan ke haifarwa ga ‘yan jihar.
Wannan hali ya kai ga tsoma bakin ma’aikatar kwadago ta kasa da uwar kungiyar kwadago ta kasa inda suka tattauna da gwamnati da kuma kungiyar kwadago reshen jihar aka samu kyakyawar fahimtar da ita ce ta kawo karshen yajin aikin da kuma sake gyara dangantaka tsakanin gwamnati da ma’aikata a jihar. Kusan wannan tattaunawa da aka yi tsakanin gwamnati da ma’aikata ta sa gwamnati ta biya ma’aikata dukkanin bukatunsu da suka hada da ci gaba da biyan tsohon tsarin albashi na shekarar 2011, aiwatar da karin girma ga dukkanin ma’aikata, biyan kudaden alawus-alawus ga ma’aikatan da sauransu.
A bangaren ma’aikata kuwa, sun amince sun dawo bakin aiki shi kuma Gwamna Al-Makura a nasa bangaren ya aiwatar da wannan yarjejeniyar ta hanyar biyan kusan dukkanin bukatun ma’aikatan kama daga biyan albashi cikakke da karin girma ga ma’aikatan jihar su sama da dubu tara, haka nan Gwamna ya bada rukunin gidaje dari biyar ga ma’aikatan jihar tare da mika musu kudade sama da naira miliyan dari da goma sha biyar ga ma’aikata su gyara gidajen, da barin ma’aikata suna zuwa zurfafa karatu yayin da suke aiki. Sama da naira miliyan dari shida ne gwamnatin ta biya a matsayin kudaden fansho ga ma’aikatan jihar da kananan hukumomi.
Su ma ma’aikatan wucin-gadi sun amfana da gwamnatin Al-Makura domin kuwa, ma’aikatan wucin-gadi dari ne gwamnan ya mayar da su ma’aikatan din-din-din. Kazalika, gwamnatin ta shigar da dukkanin ma’aikatan rusasshen kamfanin buga jarida na jihar da kuma ma’aikatan hukumar bunkasa yankin Karu (KAPDA) cikin jerin ainihin ma’aikatan jihar. Haka nan gwamnatin Al-Makura tana kokarin fara tsarin inshoran kiwon lafiya ga ma’aikatan jihar. Shugaban hukumar bunkasa kiwon lafiya a matakin farko, Dakta Mohammed Adis ne ya sanar da hakan a yayin taron likitoci na shekara-shekara wanda ya gudana a Otel din Ta’al da ke Lafia.