Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

Tsakanin Korona Da Tsaro: Wanne Ne Ya Fi Damun Talaka?

by Sulaiman Ibrahim
December 17, 2020
in NAZARI
6 min read
Tsakanin Korona Da Tsaro: Wanne Ne Ya Fi Damun Talaka?
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ya subhanallahi! Allah mun tuba Ka gafarce mu, mu muna ta murna muna shewa bako ya tafi ashe yana bayan gari ya yi likimo, ashe akwai sauran rina a kaba, sai ga shi zuwa yanzu kuma cutar kwarona tana nema ta dawo gadan-gadan kamar yadda ta faru a birnin Landan kwanakin baya, har ta kai ga mahukunta sun garkame babban birnin babu walwala da zirga-zirgar ababen hawa, duk hada-hadar da ke birnin Landan sai da ta koma kamar kufayi, kowa ya na gida a killace, kowa ya shiga taitayinsa saboda ita dai wuya mawuyaciya ce, babu kuma mai son dandana ta duk yadda take.

A nan Najeriya sai ga shi annobar tana ta kara hauhawa kamar farashin kayan masarufi, wanda kullum idan ka je shago ko kanti don sayen kaya sai ga ji sabon farashin da ya zarce na jiya; wanda dawowar wannan annoba zagaye na biyu za mu dora alhaki da laifin kowane bangare, amma laifin gwamnati ya fi yawa.
Dalili na a nan shi ne, Gwamnati ita ke karfin ikon zartas da duk wani hukunci ko dokar cewa a yi ko a bari don kare rayukan al’umma da kula da lafiyarsu, sannan hakkin gwamnati ne ta samar wa ‘yan kasa ingantaccen magani da kayan aiki don kula da lafiya. Haka zalika nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta wadata al’umma da abinci ko hanyoyin samar da abinci. Amma abin takaici da Allah wadai wannan gwamnatin da ake wa lakabi da gwamnatin baba mai gaskiya gabadaya ta ba duk wani mutum da ya kashe yini guda sukutum a cikin rana don zabenta; gwamnati ta riga ta gama ba mutanen da aka dinga yin rigima da su don kare muradun Baba Buhari.
Tun masoyan wannan gwamnati suna dan iya kakkareta har ta kai ga yanzu idan a na kalubalantar gwamnatin a gaban magoya bayanta ba su da abin cewa, daga hmm sai hmm, in ji mai ciwon hakori.
Wace iriyar azaba ce talakawa ba su sha ba a kwarona zagayen farko, to dama ana kukan targade ne, kawai sai ga karaya, sai kuma gwamnati ta garkame gari gabadaya babu wata hanya da talaka zai fita ya je don fafutikar neman abincin da zai ci kamar yadda ya sa gwagwarmayar hakan kullum, kuma dan abincin ma da gwamnati take ikirarin ta bayar don a rarraba marasa karfi da gajiyayyu, sai abun ya zamana kamar sai dan jam’iyya ake ba, sai mai uwa a gindin murhu, kuma dan wanda za a baka bai taka kara ya karya ba, sannan ba zai hanaka gobe ka nemi abincin dafawa don ci da iyalanka ba; abinci ne wanda yunwa ce da shiga wani irin hali kawai ya sa talakawa amsa saboda ba su da wata dabara dole su mika hannu su amsa.
Ashe duk da a ke wannan ma, mahandama da maha’intan wasu gwamnoni wadanda su dama babu talaka a zuciyarsu balle kuma su jikansa, sai suka tattara dukkan tallafin abinci da gwamnatin tarayya ta bayar don a rarraba wa mutane, sai suka jibge a cikin rumbu, da su raba shi har sun gwammace gara da kwari su cinye, ko kuma idan komai ya wuce su dinga bude rumbun ajiyar suna fita da shi suna sayarwa. Duk ba a fahimci hakan ba sai a lokacin da aka yi zanga-zangar EndSars, fusatattun matasa suka dinga farfasa rumbuna a wasu jihohin irinsu Kaduna, Lagos, Edo, Abuja, Filato da sauransu suna diban ganima kamar yadda suka ce.
Shin me ya sa gwamnoni ajiye wannan abinci ba su rarraba ba bayan sun san talakawa na cikin talauci da bakar yunwa da za ta iya sanya wa su aikata duk abinda ransu ke so?
Abu ne sananne cewa a halin da ‘yan kasa suke ciki a marra irin ta wannan lokaci, ba wai cutar annobar kwarona ce ta fi damun su ba, ba kuma suna kokwanto ko waswasin wanzuwar cutar ba ne, a’a akwai batutuwa wadanda sun fita muhimmanci ga rayuwa da tsarin talakan kasar nan, kuma gwamnati idan tana kaunar talakawa ne da gaske kuma da zuciya daya, ya kamata ta yi duba na tsanaki akai musamman ta fuskar tsaron rayuwar al’ummar Arewancin kasar nan, da yankin ya zama kasuwar bukatar wasu tsiraru kuma ashararun mutane. Rufe kasa ba zai haifar da komai ba illa kara sanya talakawa cikin kunci da matsin lamba a rayuwarsa.
Abun Allah wadai ne a ce gwamnatin da talakawa suka fito su ka jajirce wajen ganin sun kasa, sun tsare kuma sun raka don samun nasarar shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi wa ‘yan kasa alkawura da dama ciki har da samar da tsaro, kiyaye lafiya da rayukan al’ummar kasa amma kash!
Maimakon a karawa dabe makuba ya yi karko sai ya zamto ba ma ta sauya zani ba in ban da kara tabarbarewa da bangaren tsaron ya yi, abun takaicin ma a kodayaushe mukarraban gwamnatin ba su da wata mafita illa tura zargin ga gwamnatocin baya da niyyar boye gazawarsu a fili a idon talakawan kasa, hakan ba karamar illa ba ce da nuna gazawar gwamnatin a fili, a ce masu rike da madafan ikon al’umma suna magana irinta yan’ adawa musamman gwamnati irin ta shugaba Muhammad Buhari wadda talakawa suka dorawa amanar su akanta saboda tunanin gyara barnar da azzaluman shugabannin baya sukai wa kasar. Sai gashi gwamnatin ta na ‘political blame-game’, wanda hakan yake nuna karara babu wani mafarkin sauyi da muke zaton samu daga bangaren gwamnatin mai gaskiya, illar samar da mugun gadon ‘yan garkuwa da mutane da gaggan barayin dabbobi wanda sakacin gwamnatin ya haifar.
Talakawa sun zabi Shugaba Buhari ne domin samar da cikakken tsaron kasa ba wai gwamnatin ta rinka bamu labarin yadda tsaron ya tabarbare ba, a’a a dai samar da mafita ingantacciya, abu ne sanannen abu ne an sha yin kiraye-kirayen gwamnati akan ta sauke kafatanin hafsoshin tsaron kasar nan saboda sun kasa tabuka wani abun arziki amma shiru, abinda masu nazari suke hange kuma suke hasashe daban, abinda su kuma jami’an tsaron suke fadawa shugaban kasa don su dore kan kujerunsu daban, an ki saurarar koken ‘yan kasa akan batun, ana shashantar da maganarsu, kai su kansu jami’an gwamnati da mukarraban shugaban kasa sau tari musanta matsalar tsaron suke yi a Arewacin kasar nan, saboda haka rashin tsaro shi ne babbar damuwar duk wani talakan Arewacin kasar nan ba wai rufe kasa da sunan annobar kwarona ba..
A gwamnatance da kuma bangaren ‘yan kasuwa da talakawa tare da dalibai da sauran duk wasu al’amura na rayuwa, za mu iya cewa shekarar 2020 ta shigo kuma ga shi za ta kare a iska, gwamnati da dukkan al’umma ba su amfaneta ba, kudaden kasafin shekarar sun balbalce an rasa wuraren da aka kai su, duk hidimar annobar kwarona ta cinye, tattalin arzikin kasar ya durkushe, dama ya lafiyar kura balle ta yi hauka.
Mu dai muna kara tuni lallai gwamnati ta yi duk mai yiwuwa waurin ceto mana kannen mu wanda ‘yan bindiga suka yi gwarkuwa da su kwanan nan a kankarar jihar Katsina, kimanin dalibai ‘yan mata 600, habawa malam tamkar awaki! Tabbas gazawar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammad Buhari ta bayyana karara, kuma abun kunya ne da sakacin gwamnatin, sai dai ban sani ba ko su ma yaran kafin su je makaranta sun karbi ‘Military Clearence? Wato amincewar zuwa makaranta daga jami’an soji kamar yadda na ji mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya magantu akai lokacin da aka yanka manoma 43 na yankin Zabarmari da ke jihar Borno, ko ba mu sani ba sace daliban kusan 600 shi ma tsarawa akai domin bata gwamnatin Shugaba Buhari kamar yadda kodayaushe idan irin hakan ta faru mukarraban gwamnatin suke raina hankalin al’ummar kasa akai, na tuna wani baitin wakar marigayi Dr. Mamman Shata da yake cewa.
“Ni ina sauraron abun da tsoho ka fadi duk,
Muna ji, muna gani muna kuma sauraro..”
Allah ya kyautata makwacin Shatan waka. Mu lura cewa dalibai na zaune a gida babu karatu saboda yajin aikin da jami’oin kasar nan suke ciki, hakan ba karamar illa ba ce ga rayuwar matasan kasa; kowacce al’umma tana takama da cigaban iliminta, amma sai ga shi a gwamnatin mai gaskiya ilimin ya gagari ‘ya’yan talakawa. Shin a wannan yanayin da annobar jahilci ko annobar kwarona ya kamata gwamnati tafi mayar da hankali akai? dan karamin misali akan abun da ya faru a Arewa House a Kaduna, inda masana suka zauna domin shawo kan matsalar tsaron da ya addabi yankin Arewa, amma abun ko dadin ji babu wasu marasa kishi suka dauko ‘yan daba kusan 300 suka tarwatsa mahalarta taron wadanda suke kokarin nemawa rayuwarsu mafita, to wannan abu kadan ne cikin matsalolin annobar jahilci. A nan ba wai ina zargin gwamnati ko mukarrabanta da kitsa wannan ta’addancin ba, illa ina son in fito mana da illar jefa al’umma cikin duhun jahilci, kodayake babu mamaki tunda su dai ‘ya’yan masu fada a ji suna makarantu masu dan karen tsada, ko dai jami’o’i mallakin ‘yan kasuwa ko suna kasashen turai suna karatun su a can, saboda sun san cewa da hannunsu suka lalata tare da tagayyara tsarin ilimin kasar su.
Mu dauki gwamnatin jihar Kaduna da Kano, a yunkurinsu na kokarin dakile yaduwar annobar kwarona, a matakin farko suka sanar da ranakun rufe makarantu da jami’oin jihar kamar yadda gidajen jaridu suka rawaito, amma abun takaicin shi ne mai ya sa harkar ilimi a kodayaushe ake fara takawa? Wai mai ya sa ba za a yi wa harkar tsaron kasar nan wurjanjan ba kwatankwacin matakan da ake dauka wajen dakile annobar kwarona, idan kuwa ba haka ba, to lallai akwai wata boyayyar manufa a zukatan shugabanninmu. In ba dai dama kuna son karkatar da tunanin ‘yan kasa ba ne akan batun rashin tsaro da nuna gazawar gwamnatin tarayya a fili. Ko kuma kuna son rufe jama’a ne don shashantar da su da kawar da tunaninsu ga dalibai sama da 600 da aka sace a kankara, ko kuma kawar da tunanin dalibanmu da suka kwashe kusan wata tara a gida.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Bayanai Kan Cutar Jijjiga (Eclampsia)

Next Post

Shin Wane Irin Tallafi Shirin ‘Future Assured’ Ya Yi A Kano?

RelatedPosts

Mazan Jiya

Tunawa Da Yan Mazan Jiya: Yaushe Zai Tashi Daga Biki Zuwa Aiki? 24

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

An kirkiro da ranar tuna wa da sojoji yan mazan...

Arewa

An Yi Wa Arewa  Nisa A Kasar Nan

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Har yanzu duniyar  Arewacin Nijeriya ba mu dauka duniyar kudu...

Bayanan Sirri

Rashin Tsaro: Shugaba Buhari, Monguno Da Aikin Tattara Bayanan Sirri

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Gidado Ibrahim, Tsaro shi ne abu na farko kuma...

Next Post
Shin Wane Irin Tallafi Shirin ‘Future Assured’ Ya Yi A Kano?

Shin Wane Irin Tallafi Shirin ‘Future Assured’ Ya Yi A Kano?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version