Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYINMU

Tsakanin Nnamdi Kanu Da Sojojin Nijeriya: Kar A Bari Ungulu Ta Koma Gidanta Na Tsamiya (1)

by Tayo Adelaja
September 12, 2017
in RA'AYINMU
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Yunkurin Nnamdi Kanu na raba Nijeriya ta kowane hali na ci gaba da daukar hankali a siyasar Nijeriya. Domin a ‘yan kwanakin nan, duk mutumin da ya tsalma kafarsa cikin Nijeriya, labarin da zai fara cin karo da shi bai wuce sabuwar balahirar da ta kunno kai kan batun tsagewar kasar ba – ko ina labarin da ake yi ke nan.

Ga matasa wadanda ba su karanta tarihi ba, ko kuma dattijai wadanda suka sani amma suka take, akwai bukatar mu dan yi waiwaye kadan kan yadda abubuwa suka guda a kasar cikin shekaru 57 bayan samun ‘yancin kai.

samndaads

Samun ‘yancin kai Bayan shekaru ana yi wa kasar nan mulkin mallaka, Turawa sun mika ragamar jagoranci ga ‘yan Nijeriya a ranar 1 ga watan Oktoban 1960 domin su ci gaba da mulkar kansu.

Sai bayan shekaru biyar, watau 1966, wasu daga cikin manyan jami’an soja ‘yan kabilar Igbo suka jagorancin juyin mulki na farko a Nijeriya. Tun daga nan bala’i ya fara a kasar nan. Rayukan da aka rasa sun fi karfin misali, domin duk wani soja dan Arewa, daga kan mukamin Laftanar Kanal zuwa sama sai da aka kashe shi, ko kuma ya sha da kyar. Laftanar Kanal Yakubu Gowon (kamar yadda ake kiransa a wancan lokaci) yana cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya, domin ya yi sa’ar tserewa da gidansa. Amma sun kashe Birgediya Ademulegun, wanda shi ne Kwamanda a Jihar Kaduna.

Wancan Juyin Mulki, ya shiga kundin tarihin Nijeriya da ba za a taba mantawa da shi ba, shi ya sa wasu da yawa ke yi masa lakabi da ‘Juyin Mulkin Igbo’. Aguiyi Ironsi ya yi amfani da gibin da aka samu, maimakon ya mika mulki ga ragowar wadanda suke cikin gwamnati, wanda a zahiri shi ne abinda ya kamata ya yi, sai ya ayyana kansa a matsayin Shugaba.

Har ila yau, kabilar Igbo mazauna Arewacin Nijeriya, sai suka rika fadar maganganu masu kama da jin dadi kan kisan da aka yi wa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Arewa, lamarin da ya zama tamkar tsokana tsakaninsu da mutanen da suke rayuwa a cikinsu. Wannan na cikin manyan dalilan da suka haifar hargitsi da rashin zaman lafiya a Arewa. Lamarin ya kara kamari sakamakon kin amincewa da Aguiyi Ironsi ya yi na hukunta wadanda suka jagorancin Juyin Mulki da kashe-kashen da suka faru a 15 ga watan Janairun.

A wani yunkuri mai kama da ramuwa, manyan Sojoji daga yankin Arewa irin su Manjo Murtala Ramat Muhammad, Manjo T.Y. Danjuma da Manjo Martin Adamu, suka jagoranci kwatar mulki daga hannu Aguiyi Ironsi ko ta halin kaka, sun kuma yi nasarar hakan a 29 ga watan Yuli, 1966. Aguiyi Ironsi yana cikin mutanen da aka kashe tare da manyan sojoji ‘yan kabilar Igbo da suke da hannu a Juyin Mulkin 15 ga Janairu, 1966. Kasancewar tuni yanayi ya dumama, an samu rikici sosai a yankin Arewa, wanda ya yi sanadiyar salwantar rayukan Igbo wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.

Yakubu Gowon, wanda shi ne Shugaban Soji a Arewa, kujerarsa ita ce lamba daya ga mai sanye da Khaki, ya zama Shugaba Kasa bisa yarje masa da manya jami’ai suka yi. Laftar-Kanal Ojukwu, Gwamnan yankin Kudu Maso Gabas, ya ki amincewa da Gowon a matsayin Shugaba, inda ya nuna lallai tun da babu Aguiyi Ironsi, to wanda yake rike da mukami mafi girma a gidan soja ne ya kamata ya zama Shugaba.

Ojukwu ya kasa fahimtar cewar idan aka yi Juyin Mulki cikin nasara, mafi yawa manyan sojoji baya suke komawa, wadanda suka yi nasarar kifar da gwamnati su ne ke da cikakken ikon dora wanda zai jagoranci kasa, rashin yarda da haka ne ta sanya Ojukwu ya ayyana ficewa daga Nijeriya domin kafa tasu kasar mai suna biafra.

Yakin Basasa ya barke a ranar 6 ga watan Yuli, 1967, wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla milyoyin ‘yan Nijeriya musamman Inyamurai. A karshe dai Ojukwu ya gaza har ta kai ya gudu zuwa maboya, inda ya mika ragamar komai (sulhu) ga mataimakinsa Phillip Effiong, wadanda tare da wasu jiga-jiga a kabilar Igbo suka tunkari Gowon domin sasantawa da batun janye makamai. Daga nan, biafra ta zo karshe a Janairu, 1970.

A jawabin tarbar su da Gowon ya yi, ya furta kalmomin da kusan kowa ya dawo hayyacinsa, watau “Babu wanda ya yi nasara, kuma babu wanda aka yi nasara a kansa” su ma jagororin Igbo sun mika wuyansu ga dunkulalliyar Nijeriya. Wannan ta sa Gowon ya kaddamar da shiri na musamman wanda za a farfado da garuruwan da yaki ya tagayyara.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

BANGON FARKO

Next Post

Sanata Misau Ya Nuna Farin Cikinsa Ga Matakin Hukumar ‘Yan Sanda

RelatedPosts

Dambarwar Najeriya Cikin Shekaru 60: Murna Ya Kamata Mu Yi Ko Kuka?

Yayin Da Nijeriya Ta Cika Shekaru 60 Da ‘Yancin Kai…

by Muhammad
4 months ago
0

A jiya ne Nijeriya ta yi bikin cika shekaru 60...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Cibiyar Jinkan Tsofaffi – Minista Sadiya

Kafa Hukumar Kula Da Nakassasun Nijeriya Da Dawo Da Martabarsu

by Muhammad
4 months ago
0

A ranar Litinin, 24 ga Agusta na 2020 ne, Shugaban...

Bashin NIRSAL: Anya Talaka Na Da Rabo A Ciki Kuwa?

Bashin NIRSAL: Anya Talaka Na Da Rabo A Ciki Kuwa?

by Muhammad
5 months ago
0

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta...

Next Post

Sanata Misau Ya Nuna Farin Cikinsa Ga Matakin Hukumar ‘Yan Sanda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version