Wannan jarida ta yi amfani da karamin baki (b) a sunan ‘biafra’ saboda sam babu wata kasa biafra a yanzu, tun da hatta wadanda suka kirkiro ta sun tabbatar da hakan, idan aka waiwayi yadda suka fadi a gaban Gowon suna neman afuwa. Da babu wancan yarjejeniya da kuma afuwa da aka yi masu, tabbas da labarin ba a haka zai zo ba.
Tun da wadancan mutane sun yi mika wuya, to kokarin taso da batun biafra a yanzu tamkar sauka ne daga tsarin da magabata irin su Phillip Effiong suka taho a kai, kuma zunubi ne babba da ya kamata a tuhumi duk wanda yake da hannu a ciki da cin amanar kasa.
Bayan wasu lokuta, Shugaban Kasa Shehu Shagari ya yafewa Ojukwu tare da ba shi damar dawowa domin ci gaba da zama a Nijeriya, wannan lamari ya faru ne a 1982, watau shekaru 12 bayan tserewarsa kenan. Haka Ojukwu ya dawo ya ci gaba da harkokinsa cikin al’umma babu takura ballantana tsangwama; har ta kai ya tsaya takarar shugabancin kasa karkashin tutar jam’iyyar APGA a zabukan 2003.
Abubuwa marasa dadi sun faru, amma wasu mashirmata da ba su da labarin irin tashin hankalin da aka fuskanta na rasa rayukan mutane sama da milyan guda a yakin da sam ba shi da wani amfani, sannan a sake fitowa a bayyane ana tallata wani abu biafra. Da farko ta fara ne da MASSOB, wadda Ralph Uwazuruike ya kirkiro. Kwatsam kuma sai IPOB ta Nnamdi Kanu ta bullo tare da shan gaban waccan, wanda har ya samu damar bude haramtaccen gidan rediyo mai yada shirye-shirye mai tattare da barazana ga hadin kan Nijeriya. Duk wani zagi da cin mutunci babu irin wanda ba a yi wa sauran kabilun kasar nan a tashar Nnamdi Kanu ba.
A idanun wadanda ba Inyamurai ba, suna kallon cewar Kanu yana magana ne da yawun daukacin kabilar Igbo tun da babu wani mai karfin fada-a-ji da ya gargade shi. Wannan na daga manyan dalilan da suka sanya wasu matasa da suka kira kansu Hadakar Kungiyar Matasan Arewa bawa kabilar Igbo wa’adin wata uku su fice daga Arewa ko kuma a fitar da su, kafin daga bisa su janye.
Abin da ya yi wa mutane dadi bayan uwa’adin mai cike da tarnaki da Matasan Arewa suka bayar, shugabannin kabilar Igbo sun gano akwai dukiyarsu da ta kai adadin Tiriliyan 44 da ake hada-hada da ita a yankin Arewa. Amma abin da aka gaza yi shi ne, tun da wuri da an fadawa mutane irin su Kanu da Uwazuruike domin su san da wannan labari.
Hatta a rahoton da suka fitar game da barazanar da Matasan Arewa suka bayar, Gwamnonin yankin Inyamurai ta hannun Gwamnan Ebonyi, Dabid Umahi, ba su nuna wa Kanu da Uwazuruike kuskurensu ba. Abin da ma suka nuna shi ne, zanga-zangar da ‘Yan A Waren’ ke yi ta zaman lafiya ce.
Ana tsaka da wannan kuma kwatsan wasu matasa daga yankin Yarbawa da suka sanya wa kansu suna Matasan Oduduwa sun yi tir da batun kafa kasar biafra tare da gargadin za su fatattaki kabilar Igbo daga jihohi shida da suke yankin matukar Inyamurai ba su manta da batun kirkiro kasar biafra ba.
Koma dai mene ne ya kamata a ce akwai doka. Mutane na farko da suka cancanci a kame su ne Uwazuruike da Kanu, wadanda suka yi kunnen kashi da maganar magabantansu irin su Phillip Effiong.
Nnamdi Kanu ya saba dukkan yarjejeniyar da ta kai ga bada belinsa ba, saboda haka ya kamata a sake kama shi matukar kasar nan ta san abin da take yi. Ba a gyaran kuskure da gatari; idan har Matasan Arewa ba su janyen maganarsu ba, su ma ya kamata dokar kasa ta yi aiki a kansu.
Ba lallai ne hanyoyin gudanar da rayuwarmu musamman wajen samun daidaito ya zama iri daya ba, amma za mu iya hada kanmu, mu yi amfani da hakan wajen samar da zaman lafiya duk bambancin da yake tsakaninmu.
Kar a bari masu gigin raba kasar nan su ci nasara, domin idan aka bari wutar ta kama ba a san ranar kashe ta ba. Lallai akwai bukatar daukar matakan gaggawa gudun kar ‘Ungulu Ta Koma Gidanta Na Tsamiya.’