Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYI

Tsakanin Talakawa Da Atiku: Ana Kallon-kallo

by Tayo Adelaja
September 27, 2017
in RA'AYI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da El-Zaharadeen  Umar

Tarihin siyasar Nijeriya ba zai taba kammaluwa ba, sai da sunan tsohon matai makain shugaban Kasa, Alhaji Atiki]u Abubakar (Turakin Adamawa) saboda irin gudunmawar da ya bada asiyarsar Nijeriya, wannan  ta sa har gobe take fatan samun sauyi daga ‘yan Nijeriya.

samndaads

Yana daya daga cikin mutanan da ke son zama shugaban kasa ko ta wane hali, sai dai kuma har gobe hakkarsa bata cimma ruwa ba, sakamakon babban tabon da tsohon shugaban kasa cif Olusogun Obasanjo ya yi masa lokacin da suke akan karagar mulki.

Tsohon shugaban kasar ya rika zargin Atiku Abubakar da san kansa, da ku son tara abin duniya, wanda haka ta zama wata babbar barazana ga shi Obasanjon, kuma ta taimaka wajen kin amincewa da shi amatsayin wanda zai ga je shi a wancan lokacin.

KasancenwarAtiku Abubakar dan arewa sa ya samu farin jini a wancan lokacin da suke kafsawa da tsohon mai gidansa akan wasu dalilai da suka shafi mulki ko kuma abin duniya wanda haka ya taimakawa masa wajan shiga ga wasu daga cikin ‘yan Nijeriya.

To, amma ba anan giza ke sakar ba, tsohon mataimakin shugaban kasa ya gamu da cikas a lokuta daban-daban musamman ga talakawan Nijeriya inda suke yi masa zargi da yawa akan rashin yin hobbasa game da wasu abubuwa da suka shafi arewa  da ‘yan arewa a lokacin da suke jan ragamar mulki.

A wancan lokacin Atiku bai dauki wannan a matsayi wata barazana ba, ko tarnaki da ka iya hana shi cimma marudin shi na zama shugaban kasa, sannan hakan bata sa gwiwarsa ta yi sanyi ba, wajen ganin ya gaji tsohon maigidansa Obasonjo a shekarar 2007.

Bayan da Atiku Abubakar ya tabbatar ba zai zama shugaban kasa a wancan lokacin ba, sai kawai ya canza dibara, ta hanyar yin zamansa yana kallon abubuwan da suke zuwa suna dawo, akan abinda ya shafi sha’anin siyasa Nijeriya.

Ganin cewa yana da yara, da ya gina suka samu shiga a madafun iko, ya rika amfani da su, wajan kawo tarnaki ga bangaran Obasanjo, sai dai wani abu ya hana Atiku yin motsi mai karfi shi ne, wanda ya gaji Obasanjo kanine gare shi, domin har gobe yana zumunci da gidan su Marigayi Umaru Musa Yar’adua.

Abubuwan da har yanzu Atiku bai fahimce su a siyasa ba, su ne, ya yi wa talakawa laifin da har yanzu ba su yaf ba, sannan har yanzu bai ba su hakuri ba, kuma yana neman goyan bayan su domin cimma burinsa na zama shugaban kasar Nijeriya, kuma kamar bai shirya daidaitawa da su ba ta hanyar da ya da ce.

Kamar yadda na fada a bayan, akwai zarge-zarge akansa na siyasa, akwai wani lokacin da ake jifarsa da cewa ya taba maidawa talakawa martani da cewa ‘’Allah baya amsar Addu’ar talakan Nijeriya’’ wannan magana ba karamin tasiri ta yi a tsakanin dangantarsa da talakawa, wanda ya kamata aca ya zuwa yanzu ya gyarata an wuce wurin.

Tunda yana son takara, kuma bai yarda ya tisa keyar wani a gaba ba, domin ya cimma nasara, su kuwa talakawa suna nan a madakata domin maida martani da cewa ba a masar addu’arsu, har gobe addu’arsu  da suke Allah Yasa ya tsaya takara domin idan kere na yawo zabo na yawo za su hadu.

Lokacin da guguwar Buhari ta kada sai kawai Atiku ya shirya tsaf aka tafi da shi, da farko ya bayyana cewa ba zai yi takara ba, amma daga baya sai ra’ayi ya canza inda ya nuna sha’arwarsa ta tsayawa takara, kuma jam’iyyar mai talakawa Muhammadu Buhari, su kuma talakawa me za su yi in ba murna ba, domin kawai suna sane, ba su manta ba jira kawai azo wajan.

Hangen rashin nasarar da Atiku Abubakar ya yi na zamansa jam’iyyar ACN da PDP, ta sa, ya yi watsi da su, ya koma mutum kamar kowa, ya canza yanayi tafiyar da harkokin siyasar sa, ya rika shiga cikin talakawa domin dai kawai su yarda su kuma amince da shi, idan wani abu ya taso.

Ashe ba su manta ba, sun kagara a yi zaban fidda gwani na ‘yan takara tsakanin Atiku Abubakar da kuma sauran wadanda suka nuna sha’awarsu ta zama shugaban kasan a karkashin jam’iyyar APC ta shugaba Buhari mai talakawa.

Duk wanda ke da jahilcin siyasa a wannan lokacin ya ba kansa amsar cewa Atiku Abubakar zai yi nasara a zaban fidda gwani, saboda imanin cewa yana kudi kuma wadanda za su gudanar da wannan zabe suna bukatar kudi, saboda haka bai ji tsoron yi takara da abokan karawarsa ba, sai dai kawai ji ake yi tinjim, ya dafa kasa.

Tsayawa takara da Shugaba Buhari kadai ta isa babban laifi ga ‘yan Nijeriya domin su idon su a rufe yake inda maganar Buhari ake yi, ba su da wani zabi da ya wuce shi, saboda haka duk wanda ya ce zai ja da shi yanzu za su yi amsa hukunci.

Amma dai a bangaran ‘yan siyasa suna ganin Atiku a matsayin wani mutum mai tasirin gaske, da zai taimaka wajan ganin an yi nasara musamman ganin yana da kudi, kuma shi kansa yana da tabbacin tunda ya bada gudunmawa to akwai fatan cewa zai iya tsira  ko da daga sharrin EFCC ne idan wani abu ya so nan gaba.

Wannan tasa ya zaun a cikin APC tare da manyan yaransa da aka ba mukamai, kuma suka kara dinkewa da gwamnan jihar Adamawa, Jibrila Bindow wanda haka ya nuna cewa yanzu za a yi tafiya mai tsafta da kuma amina saboda an riga an samu nasara.

Suma ‘yan siyasar sai suka koma kamar talakawa, watau an cin moriyar ganga suka yada kwabranta, Atiku ya koma saniyar ware kamar yadda ya fada da bakinsa a siyasar Nijeriya kuma a jam’iyyar da ya ke ganin ya tallafeta ta kai ga nasara watau APC.

Saboda rashin cikar gurinsa na zama shugaban kasa wanda kuma har gobe yana so, ta sa bai yi shiru da wannan al’amarin ba, lokacin da daya daga cikin yaransa ta fito fili, ta bayyana ra’ayinta game da burin mai gidanta shi ma bai yi wata-wata ba ya kada baki ya ce jiga-jigan jam’iyyar APC sun yi watsi da shi.

Wannan fa, ina nufin manya ke nan suka yi wannan aiki, tun ba zo ga talakawa ba, wanda kila sai nan gaba wata rana za ahadu. Allah Yasa dai idan an hadu a rabu lafiya, domin wanda ke nemanka kuma yake hake da kai  tun 2007 ya hadu da kai a shekarar2019 ai sai ta Allah.

Masu fashin bakin siyasa na ganin Atiku na da niyyar taimakawa ‘yan arewa ma damar za a yi bani gishiri in baka manda. Ma’ana ko goya mani bayan ni kuma in sako maku kaya, wannan shi ne abinda ake tsammani da zaran an buda gangar siyasar 2019.

Su kuma talakawa saboda tsabar kafewa, duk da cewa Buhari bai bayyana zai sake tsayawa takara ba, amma sun ce sai shi, sannan yanzu an bullo da wani sabon yarfen siyasa ga Atiku Abubakar inda ake bayyana cewa ya riga ya shirya tsaf domin komawa gidansa na asali watau jam’iyyar PDP abinda har yanzu ba a ji daga bakinsa ba.

Abin jira a gani shi ne, tsakanin talakawan Nijeriya da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wa zai daidaita da wani ko kuwa za a ciga da kallon kallo, lokaci ne zai nuna.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Dubun Dillalin Wiwi Da Kwaya Ta Cika A Bauchi

Next Post

Kaza Da Hanjin Jimina: Me Arewa Ta Rasa?

RelatedPosts

Hon. Bello

Abinda Ya Sa Hon. Bello Kumo Ya Ciri Tuta A Siyasar Gombe

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Irin girman tasirin da Jagorori suke yi a fannonin rayuwa...

Sabuwar Shekara

Wata Mahanga Daga Jawabin Buhari Na Sabuwar Shekara

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Gidado Ibrahim, Jigo a tsarin shugabanci na Dimokradiyya shi...

Yadda Cin Zarafi Ke Neman Zama Dabi’ar Wasu ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

Yadda Cin Zarafi Ke Neman Zama Dabi’ar Wasu ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

by Daurawa Daurawa
3 weeks ago
0

Daga Usman Suleiman Sarki Mulkin dimokaradiyya tsari ne da ya...

Next Post

Kaza Da Hanjin Jimina: Me Arewa Ta Rasa?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version