‘Yan’uwa muna wa juna barka da Sallah, da fatan Allah ya karba mana ibadunmu, ya maimaita mana cikin koshin lafiya da wadata albarkar Annabi (SAW).
Da yake wannan watan da muka shiga daya ne daga cikin watannin aikin Hajji, za mu mayar da hankali a kan bayanin aikin Hajji zuwa abin da ya sauwaka kafin mu shiga wani darasi cikin yardar Allah.
Aikin Hajji ibada ne da yake da lokaci kebantacce da wuri kebantacce da ake gudanarwa. Ma’ana ba a ko wane lokaci ko wurin da mutum ya ga dama ne ba zai ce zai yi Hajji. Akwai lokaci da wurin da Allah ya kebance su da Hajjin.
Lokaci (na zamani) da ake Hajji shi ne wata guda uku, Shawwal, Zhul-kiyda, Zhul-hajji, su ne kuma ake kira da Mikati zamani. Allah (SWT) ya ce a cikin Alkur’ani: “Suna tambayar ka game da wadannan jirajiran wata, ka ce lokuta ne na mutane da suke ibadodinsu.” Don haka da zarar watan Shawwal ya kama, to an shiga lokacin da mutum zai iya yin harama da Hajji.
Kamar yadda bayani ya gabata, Hajji ba a ko ina ake daura haramar yin sa ba, yana da wuraren da Shari’a ta kebance don yin harama da shi. Duk wanda zai yi Hajji ko Umura, bai halasta gare shi ya tsallaka wadannan wuraren ba tare da ya yi harama ba.
Manzon Allah (SAW) ya sanya wa ko wadanne mutane wurin da za su yi harama (Mikati). Ya sanya wa mutanen Madina Zhal-hulaifa ya zama wurin haramarsu. A yanzu ana kiran wurin da sunan Abaru Ali. Haka nan sauran mutanen duniya da suka fara wucewa Madina ziyarar Annabi (SAW) daga ko ina a duniya, idan za su dawo Makka yin Hajji ko Umura su ma a nan Zhal-hulaifa za su yi harama. Ba za su ce sai sun koma Mikatinsu ba da aka sanya musu. Wurin yana nan daga Arewacin Madina kuma tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 450 ne, kusan shi ne mafi tsawo daga Makka a cikin sauran wuraren haramar Hajji.
Annabi (SAW) ya kafa wa mutanen Sham (Siriya) da sauran kasashe irin su Palasdin da Urdun wurin da ake kira Juhufa ya zama wurin haramarsu. Wurin yana nan a arewa-maso-yammacin Makka kusa da Radiga wadda Hausawa suke kira da Radinga. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 187. Amma tunda ruwa ya shafe Juhufa a halin yanzu, Radiga ce ta zama wurin haramar su mutanen Sham da Misra da sauran wadanda suka bi ta wajen, ita kuma tsakaninta da Makka tafiyar kilomita 204. Muma mutanen Nijeriya nan ne Mikatinmu da sauran mutanen kasashen da za su bi wurin, kamar na Yammacin Afirka.
Su kuma mutanen Najadu, Annabi (SAW) ya sanya musu Karnul-manazil ya zama Mikatinsu. Wani dutse ne da ke gabashin Makka yana kallon Arfa. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 94.
Su kuwa mutanen Yemen, Annabi (SAW) ya sanya wa mutanensu Yalamlam ya zama Mikatinsu. Shi ma dutse ne da ke kudancin Makka. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 54.
Annabi (SAW) ya kafa wa mutanen Iraki Zatu’irkin a matsayin Mikatinsu. Wuri ne da yake arewa-maso-gabas din Makka. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 94, nisan shi da Makka daya ne da na Mikatin mutanen Najadu.
Wadannan wurare da Annabi (SAW) ya kafa, su ne wuraren da mutanen duniya za su yi haramar Hajji ko Umura.
Amma su kuma wadanda suke cikin Makka (baki da ‘yan garin), a nan cikin garin ne za su yi harama. Kamar misali wadanda suke Hajjin Tamattu’i, bayan sun kammala Umura, to idan ranar da za a yi haramar Hajji ta zo, tun daga gida za su yi harama ba sai sun je wani wuri ba.
Amma idan dan cikin Makka zai yi Umura bayan Hajji, sai ya fita zuwa Tan’im kafin ya yi harama kamar yadda Annabi (SAW) ya yi umurni a kai Ummul-Mu’umina Aisha (RA) ta yi haramar Umura.
Tambihi
Batun Mikatin da maniyyatanmu na Nijeriya suke tsallakawa har sai sun je Jidda kafin su yi haramar Hajji ko Umura abu ne da yake bukatar gyara a kai.
Juhufa, Mikatin mutanen Sham shi ne Mikatin mu ‘Yan Nijeriya, amma saboda ruwa ya shafe shi sai Mikatin ya koma Radinga.
Tare Da Sayyid Isma’il Umar (Mai Diwani)
Lambar Waya: 08051529900 (Tes kawai)