Connect with us

LABARAI

Tsananin Rashin Tausayi Ne Yi Wa kananan Yara Fyade – Fatima Dala

Published

on

Mashawarciya ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, mai kula da walwalar kananan yara da hidimtawa mata ta Jihar Kano, Hajiya Fatima Abdullahi Dala, ta bayyana alhini tare da yin Allah wadai ga masu ɗabi’ar nan ta fyade ga kananan yara, wanda a halin yanzu ke ci-gaba da karuwa tamkar wutar daji.

Fatima Dala, na yin wannan jawabi ne ga mane ma labarai a bikin ranar kare hakkin dan Adam da aka saba gudanarwa a duk shekara a Ofishinta. Kazalika ta kara da cewa, tsananin rashin imani da Ilimi, rashin tausayi gami da rashin sanin darajar kai tare da mummunan son zuciya ne, suka tabbata akan masu wannan mummunar ta’ada ta fyade.

Mashawarciyar ta ce, tsabar lalacewa tare da ɓalɓancewa gami da rashin imani ne zai sa ka ga tsoho mai shekaru hamsin, ya haike wa yarinya ‘yar shekaru hudu, biyar zuwa bakwai, wannan wace irin rayuwa ce? In ji ta.

Daga nan, sai ta kara jaddada bukatar jan hankali tare da tunatar da masu irin wannan mummunar ɗabi’a cewa, su tuna hukuncin da Ubangiji Ya tanadar wa wadanda suke aikata irin wannan ɗabi’a, yana nan kuma ba zai taba canzawa ba.

Ta kara da cewa, don haka masu irin wannan aiki su ji tsoron Allah, su tuna irin
darajar da Ubangiji ya yi wa mata da kananan yara, ta ce “Ubangiji mai
tsananin azaba ne ga wanda ya saɓa masa, kuma ba zai fasa kama masu dabi’ar da laifin da suke aikatawa ba, zai hukunta su, hukunci irin wanda babu mai iya kare su ranar gobe kiyama.

Haka zalika, Dala ta yi kira tare da roƙo ga Malamanmu akan a taimaka a kara addu’a akan wadda ake yi duk da cewa, Malamai suna yin bakin kokarinsu matuka akan wannan al’amari. Amma dai himmatuwa tare da kara addu’ar, zai sa Ubangiji ya samar mana da sassauci mai yawa a rayuwar al’ummarmu.

Haka zalika ta ce, “hannu daya baya daukar jinka” dole sai an samu haɗin kan iyayen yara tare da sa hannun dukkanin al’ummar gari, sannan za a iya cimma nasara akan dakile wannan mummunar ta’ada.

Hajiya Fatima Dala, ta jinjinawa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, bisa jajircewarsa akan yakin da yake yi tare kokarin daƙile wannan mummunar ɗabi’a ta fyade a fadin Jihar Kano. Musamman ganin yadda ake tsare- tsaren yi wa tukfkar hanci, kowa ya ga irin jajircewar Gwamna wajen kwato hakkin mata da kananan yara, wadda kunshin mukaman da Gwamnan ya baiwa mata ke tabbatar da kishin da yake yi wa harkokin matan da kuma yara.

Don haka, muna ƙara shaida wa al’ummar Jihar Kano, da ma duniya baki-daya
kyakkyawan shirin daukar ingantattun matakai, wadanda tuni suka yi nisa musamman a Jihar Kano, don ganin an hukunta masu irin wannan mummunar ɗabi’a ta fyade a duk inda suke a fadin jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: