CRI Hausa" />

Tsanantar Yanayin Annobar COVID-19 A Kasashen Turai Ya Sa An Tsaurara Matakan Kandagarki

Hukumar kididdiga ta kasar Birtaniya ta gabatar da wani rahoto a jiya Juma’a, inda ta ce tsakanin ranekun 10 zuwa 16 ga watan da muke ciki, an samu karuwar kimanin mutane 35,200 masu kamuwa da cutar COVID-19 a kowace rana a yankin England, adadin da ya karu da 7,000, idan an kwatanta shi da na makon da ya gabaci wannan lokaci.
Ban da wannan kuma, wani binciken da aka yi a watan Satumban bana ya nuna cewa, kashi 9.6% na al’ummar yankin England sun taba kamuwa da kwayoyin cutar COVID-19, kana wannan jimilla ta fi yawa a yankin London, hedkwatar kasar.
Bayan sanar da wannan rahoto, wasu yankunan kasar Birtaniya sun sake kaddamar da matakai mafi tsanani na kandagarkin bazuwar cutar COVID-19.
A sa’i daya, gwamnatin yankin Lombardia dake arewacin kasar Italiya ta yanke shawarar takaita aiwatar da ayyukan tiyata a asibitocin yankin, don magance yiwuwar bazuwar cutar COVID-19. Kana daga yammacin jiya, an sake bude wani asibitin wucin gadi dake cibiyar bajekolin kayayyaki ta Milan, inda ake da niyyar kwantar da wasu mutane 6 da suka harbu da cutar COVID-19, wadanda lafiyarsu ke cikin wani yanayi mai tsanani, a cikin wannan asibitin. Ana sa ran wannan asibiti na wucin gadi zai iya daukar majiyyata 45. (Bello Wang)

Exit mobile version