Connect with us

MANYAN LABARAI

Tsangaya: Alarammomin Nijeriya Na Tare Da Dahiru Bauchi – Sheikh Hassan Musa

Published

on

Alarammomin a fadin Tarayyar Nijeriya sun bayyana goyon bayansu tare da amincewa da hada kai, domin samar da wata matsaya ta yadda za su cigaba da yin magana da murya guda, inda su ka kasance tare da fitaccen malamin addinin Islaman nan, Sheikh Dahiru Bauchi.

Jawabin haka ya fito daga bakin wanda ya jagorancin Majalisar Mahaddata Alkur’ani ta kasa tsawon shekara takwas kuma guda cikin wadanda su ka taka muhimmiyar rawa wajen ganin taron mahaddatan da a ka gabatar a Jihar Bauchi ya samu nasarar da a ke bukata, Sheikh Hassan Musa Minna.
Sheikh Hassan Minna ya kuma koka kwarai da gaske kan yadda hukumomi da gwamnatocin jihohi, musamman na Arewacin Nijeriya, ke yi wa harkar makarantun tsangaya dibar karan mahaukaciya ta hanyar bin dare a na kwasar almajirai ba tare da sanin malamansu ba, a na tafiya da su wasu wurare da ba a sani ba.
A cewarsa, wannan ba karamin keta haddin kasancewar mutum na zama dan kasa ba, wanda kundin tsarin mulki ya ba shi dama tare da kariyar zama a duk inda ya ke so a fadin Tarayyar Nijeriya.
A ta bakinsa, “kuma a fahimtar mu wannan kokari ne da gwamnatoci ke yi, domin kawar da tsarin makarantun allo a doron kasa.”
Ya cigaba da cewa, “mu a halin yanzu, ’yan tsangaya mu na jinjina wa Shehu Usman Dahiru Bauchi, wanda shi ne kusan a iya cewa, mutum daya da rage wanda a ke sauraron maganarsa kuma ya ke ta fama, domin ganin gwamnati ta sauya tunani kan irin muzgunawar da a ke yi wa almajirai, duk da cewa su ma ’yan kasa ne, kamar kowa, wadanda kundin tsarin mulki ya ba su dama kamar kowane dan kasa.
“Shehu dahiru babu shakka ya yi kira kuma alarammomi daga jihohin Nijeriya sun amsa kira, inda su ka halarci taron wuri biyu da a ka gudanar da Jihar Bauchi, inda Shehu Dahirun ya tabbatar da matsayarmu kan wannan ta’annati da a ke yi wa almajirai a Arewacin kasar nan.”
Daga nan sai ya bukaci ’yan uwa alaramomi da su yi kyakkyawan amfani tare da kyautata wa wannan bawan Allah zato, musamman ganin yadda dansa, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, ya tsaya tsayin-daka wajen tabbatar da ganin wannan taro ya samu nasara.
A karshe ya bukaci jama’a, musamman Ahlullahi, da su cigaba da kyautata wa juna zato tare da yin aiki tare domin ciyar da wannan tsari gaba.
“Hakan ta sa Shehu Usman Dahiru Bauchi ya tabbatarwa da gwamnati matsayarmu a wannan lokaci, cewar ba za mu cigaba da amincewa da irin cin kashin da a ke yi wa Alkur’ani da almajirai ba, musamman ganin alarammomi mutane ne masu kyakkyawar tarihin zaman lafiya, wadanda ba sa rigima da kowa, sannan kuma ba irin gudunmawar da ba su bai wa wannan gwamnatin ba a lokacin da ta ke hakilon samun ragamar jagorantar kasar nan ba,” in ji shi.
Daga nan sai ya yi addu’ar fatan Allah ya kara wa Shehu lafiya, duk wadanda su ka halarci wannan taro na kusa da nesa kuma ya yi addu’ar fatan kowa ya koma gidansa lafiya, sannan ya bukace su da kowa ya zauna cikin shiri, domin aiki yanzu a ka fara.
“Mu na kara jadadda wa gwamnatin aniyarmu ta karbar duk wani gyara da bai ci karo da cin zarafin Alkur’ani da masu neman sa ba,” a ta bakin alaramman.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: