Tsangwama Daga Jam’iyyar APC Na Kara Wa Sanata Saraki Farin Jini Ne —Sanata Hamma Misau

Pic.24. Senate President, Bukola Saraki (R); with the former Governor of Borno State, Alhaji Ali Modu Sheriff at Al-Nur Mosque, Wuse 2, during the Funeral Prayer for the Former Minister of Finance, Mallam Adamu Ciroma in Abuja on Thursday(5/7/18). 03620/5/7/2018/Anthony Alabi/NAN

Shugaban kwamitin Majalisar Dattijai a kan sojojin ruwa, Sanata Isah Hamma Misau da takwaransa mai kula da kwamitin Majalisar Dattaijai a kan bankuna da cibiyoyin kudade Sanata Rafiu Adebayo Ibrahim sun bayyana cewa, yadda shugabannin jami’iyyar APC ke gudanar da lamarin sauya shekar da shugaban Majalisar Datijjai Dakta Bukola Saraki ya yi, yana kara masa farin jini ne a fagen siysar kasar nan baki daya.

A wata sanarwa da Sanatocin su biyu suka sanya wa hanun, sun kalubalanci jami’iyyar APC a kan yadda ta mayar da hankalinta gaba daya a kan mutum daya maimakon ta mayar da hanalinta a kan yi wa ‘yan Nijeriya bayanin hakikanin aiyyukan da jami’iyyar ta gudanar wa ‘yan Nijeriya a cikin watanni 38 da suka wuce tun daga lokacin da jam’iyyar ta dare kan karagar mulkin kasar nan.

“Wannan shi ne karo na farko a tarihin Nijeriya da jam’iyya mai mulki za ta bar maganar tattauna abin da ta cimma na aiyyuka, ta koma mayar da laifin rashin samun nasarar ta a kan mutum daya kwal. Wannan shi ne karo na farko da jami’yya mai mulki za ta labe da cewa dukkan matsalolin da ake fuskanta a kasar nan laifin wani mutum daya shi kadai.

“Jami’yyar APC ta bata dukkan lokuttan shugaban jami’yyarta da jagoran jam’iyyar da sakataren watsa labaranta da sanatoci 2 da kuma masu bai wa shugaban kasa shawara a kan zagi da cin mutuncin shugaban majalisa a kullum rana ta Allah, abin yana kokarin ya zama kamar Saraki ne kadai dan siyasa a fagen siyasar Nijeriya,  har sun mayar da sunan Saraki ya zama abin ambato a kullum a siyasar Nijeriya. In har da wadanna mutane za su mayar da kokarinsu zuwa hanyoyin neman mafita ga kasa, musamman matsalolin da suka shafi tattalin arziki da rashin tsaro da sauransu to da sun fito hanyoyin fita daga cikin matsalar amma suna bata lokacinsu a kan abin da ba zai taimaki kasa ba.

“Mun yi mamakin cewa, a halin yanzun dukkan shawarwarin da Majalisar Dattaijai ta yanke a na dora wa a kan Saraki shi kadai, to a ina za a dora dukkan nasarorin da Majalisa ta samu na kyawawan dokokin da ta zartas a zamani shugabancin Dakta Bukola Saraki?

“A kan haka muke gargadin jami’yyar APC da cewa, mu ‘yan jam’iyyar PDP mun isa fuskantar duk matsalar da ake shirya aukarwa in majalisa ta dawo zamanta, babu barazanar da zai sa mu ja da baya.”

Sanata Isah Hamma Misau, Sanata ne mai wakilitar jihar Bauchi da Sanata Rafiu Adebayo Ibrahim daga jihar Kwara na daga cikin manyan sanatoci masu goyon bayan Sanata Saraki, kuma suna daga cikin wadabda suka canza sheka daga jami’yyar APC zuwa PDP kwanan nan.

Exit mobile version