Sani Tahir" />

Tsaraba Daga Tsohuwar Marubuciyar Da Ta Fara Rubutu A 1977

HAJIYA AISHA MUSA ISAH, uwa ce kuma marubuciya da ta hau matakin shugabanci a kungiyoyin marubuta, ta ga jiya sannan tana ganin yau. A wannan tattaunawa da ta yi da SANI TAHIR, ta yi bayanai a game da rubutu da alfanunsa tun a tsohon zamanin da ya shude da kuma na yanzu, kana ta ba da shawarwari ga marubuta masu tasowa. Ga tattaunawar:

 

Ki fada wa masu karatu sunanki da tarihin rayuwarki a takaice…

To bismillahir’rahmanin rahim, da farko dai sunana Aisha Musa Isah. An haife ni a shekarar 1954 a watan biyu, na taso a gidan mu, muna da yawa, inda aka saka ni a makarantar allo da islamiyya, Alhamdulillah a makarantar allo na kai matakin sauka, da safe mu je makarantar islamiyya da yamma kuma mu je allo, saboda ni a lokacin ba a saka ni makarantar boko ba saboda wani dalili na wannan lokacin ba a dauki ilimin boko da muhimmanci ga ‘ya’ya mata amma kuma ‘yan’uwana maza suna yin boko. Aka yi min aure a 1968, aka ba ni mai gidana tsohon ministan ilmi na jamhuriya ta biyu lokacin Shehu Shagari Alhaji Bilyaminu Usman Hadeja. Ina alfahari shi ne mijina na farko muna tare da shi sama da shekara arba’in sai mutuwa ce ta raba mu da shi.

A duk da ban yi karatun boko ba amma duk wanda ya karanci arabiya ya ce zai yi karatun boko, musamman ma idan mutum marubuci ne zai karanta ya rubuta to da ka koma bangaren boko ba zai yi maka wahala ba. Saboda ni a gidan ‘yan boko nake sai na samu kwarin gwiwa aka taimaka min, meye taimako jaridun mu na wancan lokacin Gaskiya Tafi Kwabo ce, sai aka yi min rajista da su kamfanin jaridar inda nake samun kwafin jaridar duk ranar litinin. A nan ma na samu damar iya karatun boko. To sai na fara karanta littafai kamar su Magana Jarice, Ruwan Bagaja, da littafin Wakokin nan na su Mu’azu Hadeja. To sai nake tinanin tun da na iya karantawa da rubutawa me zai hana in fara rubutawa ni ma, sai na shiga rubutu, in rubuta a gida in bayar a duba da haka har na rubuta littafina na farko a aalif 1977, a lokacin duk arewa babu madaba’ar buga littafi sa a Zariya (Madaba’ar NNPC, watau Northern Nigeria Publishing Company), a lokacin babu waya sai dai kawai ta gidan waya mutum zai tura, har muka saba da su a haka. Inda na fara samun sanyin gwiwa da su shi ne da na tura littafina sai suka ce min ya yi wa ‘yan sakandire kadan kuma ya yi wa ‘yan firamare yawa, aka dawo min da littafin domin in kara ko in rage.

Na rasa yanda zan yi, kawai sai na bar su saboda abu ne mai wahalar gaske ka gama rubuta littafi a ce maka ka rage ko ka kara. A alif 1978, Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna suna wani shiri mai suna shafe labarin shuni, inda suke karanta littafi duk wata uku idan suka gama za su hada na watanni uku su yi jarabawa, to a nan littafin nawa a wata ukun farko ya zo na daya, suka ba ni kyautuka.

Ko za ki fada wa masu karatu adadin littafanki da suka shiga kasuwa?

Littafaina da suka shiga kasuwa ba su da yawa, guda hudu ne: Su Waye Khulafa’ur Rashiduna, Ya’ya Mata, Wankan Gawa da Likkafani, Tarbiyar Yara a Musulunci. Amma kuma rubuce-rubucena suna da yawan gaske.

 

A wacce shekara wadannan littafai suka fita kasuwa?

Na farko daga shekarar alif dubu biyu da biyu (2002), sai sauran duk a shekarar 2015 suka fita.

 

Wane irin kalubale kika fuskanta a harkar rubutu?

An fuskanci abubuwa da yawa don duk wanda yake rubutu, ya san meye rubutu ya san akwai kalubale da yawa ma. Don littafina na farko Khulafa’ur Rashidun da na yi na kai wa babban limamin Hadeja na yanzu Malam Abdulrahman ya duba domin ya yi min gyara a kai, wallahi shafi biyu ya kewaye da jan biro, ya soke ya ce shafi biyun nan be gamsu da su ba, ko na cire ko na gyara. Na ga na riga na gama fa na kai mai ya yi gyara, ai da na ajiye littafin ya fi wata shida ban sake bi ta kansa ba, na sha wahala a wannan lokacin. Kalubale da yawa wani lokacin babu kudin da mutum zai buga littafi, wani lokacin ka kai gurin bugawa nan ma wani kalubale ne, don a kwai wata shekara da aka sami matsalar wutar lantarki wallahi sai da littafi ya makale a madaba’a ya fi wata uku sannan ya fito, ka ga wannan kalubale ne.

 

Kina da shawara ga marubuta masu tasowa?

Akwai shawara da zan ba wa marubuta masu tasowa, su sani don shi fa rubutu dan hakuri ne da juriya, kuma shi rubutun littafi yana bukatar bincike, don shi ba kamar yadda za ka rubuta kirkirarren labari ba ne. Saboda gaskiya wani abun sai ka yi rubutun ka zo kana dubawa za ka ga wani abin be ma dace da ka sa ba, sakamakon rashin bincike da ba ka yi ba, gaskiya marubuci ya kasance yana karance-karance, nazari, tambaya a kan abin da za ka rubuta, ba ma sai za ka rubuta littafi ba abun da ka ga zai maka amfani ka rubuta ka ajiye don wata rana.

 

Tsawon lokacin da kika kwashe kina rubutu, menene ya fi birge ki?

Abubuwa da dama suna birge ni a game da rubutu, kuma na yarda da aka ce alkalami ya fi takobi, na yarda da wannan karin maganar da hausawa suke fada. Duk iliminka in ba kana rubutu ba a boye kake, wani ba zai san da kai ba, abin da yake kara birge ni game da rubutu shi ne har yanzu wani can zai dauki abin da ka rubuta ya karanta ya bugo maka waya, yana jin dadi da farin ciki saboda rubutunka ya yi amfani da shi. Lokacin da littafin Khulafa’ur Rashidun ya fita, akwai masu kirana a waya suna nuna farin ciki wallahi na rubuta sama da mutum dari biyu (200), ka ga wannan ba karamin abun burgewa bane. Akawi wanda daga Jihar Taraba ya kira ni yana ta yi min addu’a wanda har yanzu ina alfahari da rubutu. Za a kira ka idan za a yi taro a ce ka zo ka yi bayani ka gabatar da takarda a gurin saboda mutum yana rubutu wannan ba karamin abun burgewa ba ne to gaskiya abubuwa sun burge ni a rubutu sosai.

 

Hajiya za ki ga wasu marubutan suna da layin da suka dauka wajen rubutu, misali wasu suna rubutun yaki ko soyayya, wasu kuma siyasa, to ke a cikin wanne kike rubutu?

To, alhamdulillah ni dai rubutuna gaskiya a kan addini na fi yi, akwai dalilai da yawa da na juya a kan addini tun da shi ilimin addini in ka yi rubutu fa, ba kai ne ka kirkiroshi ba, dole karantawa ka yi a gurin wani malamin. Ka je ka bibiya yanda abun yake ka rubuta, to sai ka ga da ka je kana kirkirar abin da al’umma za su dinga yin Allah wadai da wannan, gwara ka rubuta abin da al’umma za su karu. Don wallahi littafin Khulafa  wani malami ya bugo min waya yana cewa da ni a cikin tarihin Sayyadina Usman akwai gurin da ya dade bai fuskanta ba sai da ya karanta littafina sannan ya gamsu da abin da yake nema, shi ya sa na fi karkata ga rubutun addini.

Kuma ni uwar ‘ya’ya mata ce nake ganin babu tarbiya kamar da za ka yi mata irin a kan addinin musulunci, duk wasu abubuwa za ka ga cikin ikon Allah ta shallake sharrin zamani. Wannan shi ne dalilina, haka su ma masu rubutu a kan soyayya ko yaki, ban kalubalance su ba, rubutu; rubutu ne suna yin kokari sosai, amma kuma akwai abubuwan da ya kamata a yi musu gyara kamar su masu rubutun soyayya gaskiya wani abun bai kamata su ringa rubutawa ba, saboda wani abun bai dace yarinyar da ba ta mallaki hankalinta ba ta dinga karanta abin da bai kamata ba don ta iya karatu, ko abin da ta ji don gaskiya duk yadda ka kai da kokarin ganin cewa da kwana sai ka sanya ta yi maka tambaya, to ka ga in ka rubuta ‘yarka ta dauka ta karanta ai sai ta dauko wanda ya fi naka tana karantawa, ka ga ai sai ta fi haka lalacewa shi ya sa wannan dalilin naki na koma bangaren rubutun addini.

 

Ya alakar HajIya da sauran marubuta?

Ina da alaka da marubuta don ko a can Hadeja, ni ce shugabar marubuta mata ta karamar hukumar Hadeja, kuma ina cikin kungiyar marubuta karamar hukumar Hadeja ta kasa, ‘yar kungiyar marubuta ta kasa, reshen jihar Kano wato (Association of Nigeria Author ANA), don ko kwanakin baya da wani dan babura ya rubuta tarihin Sarkin Hadeja da za kaddamar da littafin aka ce min in rubutu daga bangaren marubuta, na yi don a karanta a gurin taron bikin aka ba ni dama na yi magana saboda an tara sarakunan arewa, gaskiya ina da alaka da marubuta mai karfi.

 

Ba shikenan hirar ba, a mako mai zuwa za mu ji batutuwan da suka shafi lalacewar matasa da abin da ya shafi tarbiyyar yara da yadda iyaye suke sakaci har ake wa ‘ya’yansu fyade. Ta kuma ba da shawarar a rika yanke wa masu yi wa yara fyade hukuncin kisa domin ya zama darasi ga masu aikatawa. A tare mu a mako mai zuwa!

 

Exit mobile version