Tsaraba Ga Magidanta Kan Biyan Hakkin Aure

Daga Edita.

A makon da ya gabata mun samu tangarda wurin rubuta shafin da wannan rubutun ya cigaba, don haka muna baiwa masu karatu hakuri sannan muna godiya ga wadanda suka bugo mana waya don neman sake maimaita rubutun, mun amshi bukatarku, don haka ga maimaicin rubutun a halin yanzu:

Dangane da yawan tes da wayoyi da muke yawan samu wasu mata ne suke kawo kukan rashin dadewan mazajensu a shimfida wasu kuma mazan ne ke kukan rashin kuzarin su, to in dai ana so a kiyaye sai an hakura da cin wasu ababen.

A saboda haka ne ma dukkan bangarorin da ke da hannu wajen ganin an samu lafiyayyiyar dangantakar zaman aure mai gamsarwa ke kokari iya kokari wajen ganin daga bangarensu ba a samu matsala ba.

Mijin zai yi kokarinsa wajen ganin ya tsira da mutunci, girma da darajarsa wajen ganin bai tauye matarsa ba a wannan bangare, haka ita ma matar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ta gamsar da maigida a duk lokacin da aka zo tarawa

Wannan kokari da musamman maza ke yi shi ke sanya su a lokuta da dama shaye-shaye abinda suke kira da maganin karfin maza. Wannan kuwa na iya zama na turanci (Biagra) ko na Hausa, irin wadanda za ka ji masu tallan magani a kan tituna da kasuwanni na kwarmata tasiri da ingancinsu

Sai dai kuma, wadannan magunguna na karfin maza na da matukar illa na kai tsaye ko dai a nan gaba ko kuma a nan take. Misali, maganin karfin maza na turanci na bayar da kuzari da karfi ga namiji a lokacin da ya sha, amma illarsa shi ne: zai kasance idan har mutum ya saba da shansa, in har bai sha ba, ba zai iya tsinana komai ba. Na biyu kuma shi ne, zai takaita rayuwar jima’in mutum.

Shi kuwa maganin Hausa dama dai babu wani bincike mai zurfi da aka yi a kai bare a gane adadin da za a sha da zai zama bai yi wa jiki yawa ba. Kuma za ta iya yiwuwa akwai wani adadi na guba a jikin ganye, saiwa ko sassaken maganin da ya kamata a ce an yi waje da shi kafin a sha mai amfanin, amma sai mu dirkawa cikinmu daga bisani wancan guba ya taru ya haifar da wata lalurar ta daban.

Mafita…

Sau tari abin da ke sanyawa namiji ya gaza wani katabus na a zo a gani a yayin kwanciyar aure na da nasaba da irin abin da ya ke ci. Maza ya kamata ku fahimci cewa wadanan nau’ika na abinci na da tasiri wajen dakile mazantakarku kuma da zarar kun cire su daga jerin cimarku na yau da kullum, to fa ba sai kun sha wani maganin karfin maza ba, kuma matayenku za su yi murna da ku, kuma har lau babu wata fargaba ta samun matsalar lafiya sakamakon kokarin mutunta gida

Ga nau’ikan abinci da za ka cire daga jerin abincinka ko kuma ka rage su matukar ragewa

 

  1. Kayan Toye-Toye

Nau’ikan abincin da aka toya, kamarsu dankali na Hausa da turawa, kayan fulawa da dai sauran abubuwan da ake toya su da mai wanda suke rage karfin sha’awar namiji, kai har ma da mace kamar yadda wani bincike na lafiyar jima’i ya tabbatar,

A cewar binciken, kayan toye-toyen na nakasta maniyyin namiji ta yadda hakan zai tasirantu wajen hana samun mikewar mazakutarsa yadda ya kamata ko da kuwa an yi masa shafa na sha’awa.

 

  1. Nau’ikan abincin da ke dauke da sinidarin ‘Carbohydrate’.

Wadannan nau’ika na abinci sun hada da gyararren shinkafa da muke kira da shinkafar gwamnati, (shinkafar gida ta fi amfani ga lafiyar jiki da na jima’i). Sauran abincin da ke dakushe kaifin mazakuta sun hada da ababaden da ake sarrafa su daga fulawa kamarsu burodi, cin-cin, fanke da dai sauransu. Taliyar Indomie da sauran taliyoyi da makaroni duk na iya dakushe kaifin mazakuta musamman idan aka juri cinsu kullum da kullum

 

  1. Nau’ikan Lemukan Gwangwani da na kwalba da na jarka

Lemukan na dauke da wani adadi na sikari sama da yadda jiki ke bukata, shi kuma illar sukari na da matukar yawa a jikin Dan Adam. Da farko dai sikari na kara wa mutum kiba, ita kuma kiba na hana namiji kaiwa da komowa a yayin jima’i. Abu na biyu game da sikari dangane da lafiyar al’aurar namiji shi ne, sikari na hana jijiyoyin da ke harba jini zuwa mazakutar namiji a lokacin da yake bukatar haka sai su yi sanyi.

Sikari ke jawo matsalar nan da ake kira da illar sikari wato ‘Sugar Crash’ a turance. Idan wannan matsala ta faru, duk tabawar da mace za ta yi wa namiji ba zai mike ba ko da kuwa yana so a ransa ya yi jima’i.

 

To, mazaje, sai a kula wajen tantance mai za a ci don a tsira da lafiyar jiki da lafiyar aure. Mu hadu a mako mai zuwa cikin yardarm Allah.

Exit mobile version