Tsarin Albashin IPPIS: Gwamnatin Tarayya Ba Za Ta Bi Umurnin Kotu Ba – ASUU

A jiya ce, Kungiyar malaman Jami’o’i ta ASUU, ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya ba za ta bi umurnin kotu ba ko da kungiyar ta sami umurni daga kotun a kan warware matsalar nan ta tsarin biyan albashi na IPPIS.

Kungiyar ta ASUU ta musanta zargin cewa wai tana goyon bayan almundahana ne a inda ta ki ta shiga tsarin albashin na IPPIS, tana mai bayanin cewa kiyawar da take yi tana yin hakan ne a bisa kan doka, ‘yanci da kuma damar da malaman Jami’o’in  suke da ita wacce tsarin ke neman rusawa.

Kungiyar na fadin hakan ne a bisa abin da ta kira da labaran karya da gwamnatin tarayya ke baiwa al’umma a kan zargin da take yi na kin shigar da sama da Malaman Jami’o’in 39,000 a tsarin albashin na IPPIS.

Bayananin hakan yana kunshe ne a cikin maganar shugaban kungiyar malaman Jami’o’in ta ASUU, a Jami’ar Ibadan, Farfesa Deji Omole, a Ibadan, ya yi.

Sabanin abin da gwamnati ke nunawa, kungiyar ta ASUU ta yi zargin cewa tana da cikakken goyon bayan sama da kashi 90 na wakilanta.

Omole ya ce: “Ba mu taba samun kanmu a matsala irin wannan ba. gwamnati ce an rantsar da ita a matsayin gwamnatin farar hula, amma ba ta da alamomin gwamnatin da ke bin dimokuradiyya ta kuma ki duk wani abin da ya shafi sulhu da sasantawa; gwamnatin da ba ta iya biyan hakkin Ilimi, gwamnatin da ta ke kin bin umurnin kotuna, wannan ne ya sanya ba mu yi tunanin kai wannan gwamnatin kotu ba a kan batun tsarin albashin na IPPIS domin muna da tabbacin gwamnatin ba za ta bi sakamakon umurnin da kotun za ta bayar ba.

“A yanzun wannan gwamnatin ta zama kwararriya wajen yada labaran karya ta hanyar daukan wasu malaman Jami’o’in bogi. Dukkanin wakilan kungiyarmu suna tare da uwar kungiyar mu. Muna fada ne a kan gaskiyarmu, mun kuma samu nasara a kan gwamnati. Amma suna nan a kan bukatar su, sun kuma lula a kan kin bin doka.”

Exit mobile version