Tsarin Ci Gaban Nijeriya: FCDA Ta Himmatu Wajen Kammala Abubuwan More Rayuwa A Idu

Daga Idris Aliyu Daudawa

Yayin da ake ci gaba dayin dukkan abubuwan da suka dace saboda dawo kimar ta da komadar ci gaban tattalin arziki na Nijeriya, ya kuma kasance an ya koma dai dai dana sauran sassan Nijeriya.

Hukumar babban birnin tarayya ta ba masu zuba hannun jari tabbacin cewar, a shirye take domin ta ga cewar, ta kammala cikin lokaci, abubuwan more rayuwa a sashe na biyu wurin shakatawa na masana’antu dake Idu. Wannan kuma shi zai sha masu sha’awar zuba hannun jari na gida dana waje.

Ministan babban birnin tarayya Malam Muhammed Musa Bello shi ne wanda ya bada wannan tabbacin ranar Talata, a Abuja Sheraton Hotel.

Ministan babban birnin tarayya Malam Muhammed Musa Bello shi ya bada wannan tabbacin ranar Talata ta wannan mako, a ranar babban birnin tarayya Abuja, a wurin taron ci gaban tattalin arziki da kuma tsare tsaren yadda za a cimma kai gaci, wanda aka yi a Hotel din Sheraton.

Bugu da kari tawagar babban birnin tarayya a wurin taron ta kunshi, Sakataren din din din Mr Chrisrtian Chinyeaka Ohaa, Sakataren babban birnin tarayya Engr Umar Gambo Jibrin, Shugaban ma’aikata Bashir Maibornu, da kuma sauran manyan jami’ai, sun tattauna da masu zuba hannun jari, ba domin komai ba, sai saboda idan akwai wasu matsaloli, wadanda zasu iya kawo cikas, ayi maganinsu, saboda kada su hana masu sha’awar zuba hannun jari zuwa.

Babba daga cikin masu sa hannun jarin shi ne Zeberced wanda dan kasar Turkiyya ne, wanda  a halin yanzu yana yana gina kashi na biyu na filin masana’antu na Idu, wanda fili ne mai hekta 245, ana sa ran zai samar da fulotai 170 na kafa masana’antu, wadanda masu zuba hannunn jari daban daban, da suka hada da yin kayayyaki, sayar da kayayyaki, kasuwanci , da kuma samar da dubban ayyuka.

Shi dai taron ya gano wata hanya wadda ba a kammala ba,. Wadda zata kais u masu zuba hannun jarin zuwa filin masana’antun, abin da suka fahimci yana daya daga cikin abubuwan da zasu kawo matsala ga masu sa hannun jari.

Ministan babban birnin tarayya da kuma Ministar kasafin kudi, da kuma tsare tsaren manufofin kasa, Zainab Ahmed, sun amince da zasu yi aiki tare, wajen samo kudaden da za a kammala ita hanyar.

Fahimtar junan da aka samu tsakanin shi Zeberced da kuma su Ministocin biyu, hakan ya bada dama wajen samun makamar zaren, domin shawo kan al’amura, wadanda suka shafi sauran masu son zuba jari, saboda suma sun bayyana al’amuran da suke sha masu gaba.

Manyan masu zuba jari a Hukumar lafiya ta duniya, kamfanonin harhada magunguna wadanda aka amince dasu, kamfanin iskar gas, kamfanonin da suke yin takalma, duk sun bukaci da a basau filaye, domin su kafa masana’antun su, duk an hada su da shi wanda yake lura da gina wurin saboda su suna sha’awar dawo da masana’antunsu.

Ministan babban birnin tarayyar ya umurci Kamfanin zuba hannun jari wanda ake kira Abuja Inbestment Company, dasu gaggauta tabbatar da cewar, masu sha’awar zuba hannun jari, wadanda suka nuna sha’awarsu ta a basu fili a Abuja Technology Billage (ATB) , an basu dukkan gudunmawa da kuma shawarwarin da suka kamata.

Ma’aikatar kasafin kudi da tsare tsaren kasaita ta shirya taron , wanda kuma shi ya bayyana dalilai uku na shirya shi taron, na farko shi ne a dawo karfin ci gaban tattalin arziki, kamar yadda yake a da, da a kalla kasha 7 cikin dari nan da zuwa shekara ta 2020, su sa hannun jari a Nijeriya, wannan kuma shi taimakawa ‘yan Nijeriya samun  dadi zaman rayuwarsu, da kuma habaka shi tattalin arzikin.

Exit mobile version