Tsarin Karba-Karba A Neja: Dan Majalisa Ya Gindaya Sharudda

Neja

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

 

Jihar Neja na daga cikin jahohin da suka amince da tsarin karba karba na kujerar gwamnan jiha. Tsarin wanda aka faro shi tun dawowar tsarin mulkin dimukuradiyya a shekarar 1999, da jam’iyyar PDP a wancan lokacin ta amince da shi ne ya baiwa yankin Neja ta kudu da aka sani da Zone ‘A’ damar rike kujerar tsawon shekau takwas.

Duk da cewar a zango na biyu da gwamnan lokacin Injiniya Abdullahi Abdulkadir Kure ya nemi zarcewa ya samu togiyar rashin amincewar wani zagin PDP a lokacin, inda suka canja sheka zuwa PRP inda Injiniya Mustapha Bello daga yankin Neja ta arewa ( Zone C) ya nemi kujerar bayan ficewarsa daga PDP din zuwa PRP, duk da gumurzun da aka yi a siyasan ce da kar da shudin goshi jam’iyyar PDP mai mulki a lokacin ta iya kai banten ta inda Injiniya Abdullahi Abdulkadir Kuren ya sake samun dama ta biyu zuwa 2007.

Bayan kammala wa’adin Injiniya Kuren, yankin Neja ta tsakiya ta samu nasarar karban mulkin, inda Dakta Mu’azu Babangida Aliyu daga Neja ta tsakiya ( Zone B) ya samu darewa bisa kujerar gwamnan har zuwa shekaru hudu, inda lokacin da ya nemi dawowa karo na biyu, ya samu togiya daga jam’iyyar CPC a lokacin, wanda Barista Bako Shatima da ke shugabantar jam’iyyar ya samu fagen shiga takarar daga jam’iyyar CPC din duk da cewar ya fito ne daga yankin Neja ta kudu ( Zone A) shiyyar da ta jagoranci jihar tsawon shekaru takwas din farko bayan dawowar mulkin dimukuradiyyar.

Hakan ya razana gwamnatin lokacin inda sai da suka nemi Baristan ya janye bisa wasu sharuddan da ya gindaya, wanda rahotanni sun tabbatar da cewar dan takarar na CPC din a lokacin bai amincewa janyewar ba saboda goyon bayan talakawan jihar da yake da shi.

A daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulkin jihar ke shirye shiryen fuskantar zabukan 2023, tana fuskantar kalubalen cikin gida akan wannan kudurin na karba karba inda take kokarin tsarin ya cigaba.

A wani zaman masu ruwa da tsaki da jam’iyyar APC ta gudanar a makon da ya gabata, ta sake jaddada wannan kudurin na sake baiwa yankin Neja ta kudu ( Zone A) damar sake rike wannan kujerar ta gwamna a zaben 2023 mai zuwa.

Duk da wannan matsayar ta jam’iyyar APC din, dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Suleja, Tafa da Gurara, Hon. Abubakar Lado Suleja ya nuna turjiyarsa akai, inda ya nuna cewar lallai a zaben 2023 ba bu abinda zai hana shi takarar kujerar gwamnan ba muddin ba a bi ka’idar da ta dace ba.

A cewar dan majalisar, gwamnatin jihar da ake zaba na kasawa ne saboda rashin zaben mutanen da suka dace, musamman wadanda ake daukowa su ci zabe mutane ne da ba su wahala da jam’iyya ba, kuma ba su san matsalolin jihar ba.

Hon. Lado yace bai kamata jam’iyya ta fara maganar wanda zai gaji kujerar gwamnan jihar ba a yanzu ganin lokacin zaben bai yi ba, balle maganar karba karba ya taso.

Ya cigaba da cewar zuwa yanzu jam’iyya ta kasa zaben shugabannin jam’iyya, balle ta fara tunanin shiyyar da ya kamata ta gaji kujerar gwamnan. Sabbin zababbun shugabannin jam’iyya da aka zaba suke da alhakin yanke hukuncin cigaba da tsarin karba karban ko rusa shi.

A wata takardar da dan majalisar ya fitar, ya jawo hankalin mutanen yankin Neja ta kudu da kar su amince da kakaba masu dan takara daga waje idan ma tsarin zai cigaba, yace idan yankin zasu fitar da asalin Banufe cikakken dan siyasa, mazauni Minna, wanda yasan halin da jama’ar jihar ke ciki a shirye yake ya janye takararsa.

Dan majalisar, Hon. Abubakar Lado Suleja, da ya fito daga yankin Neja ta tsakiya, ya ziyarci masu ruwa da tsaki a yankin da mafi rinjayen su Nufawa lokacin da wasu matasa suka karrama shi da lambar yabo a masarautar Bida a lokacin bukin ranar Nupanci na wannan shekarar da ya gudana a watan jiya, inda ya bayyana masu kudurinsa na yin takarar kujerar gwamnan a zaben 2023 mai zuwa.

Manazarta da dama na da ra’ayin cewar jihar ta kasa samun cigaba ne musamman ganin yadda ake kakabawa al’umma dan takara daga waje musamman wadanda ba wani rawar kirki suke takawa a siyasar jihar ba, wanda hakan ya sa ba su cika damuwa da halin da jihar da al’ummarta ke ciki ba.

Sau tari zaben kujerar gwamnan Neja ya ta’allaka ne akan na wa ka ajiye kuma wa ka ke da shi, wanda kusan masu darewa kan kujerun ba sanannu ba ne a siyasar jam’iyya, wanda ko bayan an kafa mulkin ba kasafai ake baiwa ‘yan siyasar da suka taka rawar gani wajen kafa gwamnatin ba damar taka rawar da ta dace ba, da zai taimakawa gwamnatin samun nasarar ciyar da jihar gaba ba.

Exit mobile version