Tsarin Leadership Ya Burge Ni – Dan Malikin Progress Fm

Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Alhaji Babangida Usman Mai Atamfa, Dan Malikin Progress FM Gombe, ya bayyana cewa, sabon tsarin da Jaridar Leadership A Yau ta bullo da shi tsari ne da zai burge kowa, musammam masu karanta jarida, inda ya ce, ita ce jaridar Hausa ta farko da ta fara fitowa kowacce rana kamar jaridar Turanci.

Alhaji Babangida Usman ya ce, gyare- gyaren da LEADERSHIP ta yi, wanda ya sha bamban da sauran, shi ne zai barawa duk wani mai sha’awar karanta jaridar jin dadin karanta ta, saboda wannan tsarin abin a yaba ne.

Ya ce, “bobarin kawo labarai masu muhimmanci wanda ya shafi kowanne bangare na rayuwar dan adam na daga cikin abinda ya sa jaridar ta sha bamban, amma ya na da kyau a sake bullo da wasu shafuka da za su ilmantar, kamar a cikin shafin da kiwon lafiya a samu masani ya na amsa tambayoyin masu karatu.”

Dan Malikin Progress FM Gombe ya yi amfani da wannan damar wajen bai wa hukumomin jaridar shawarar cewa maimakon fitowa kowacce rana, da kamata ya yi a ce za ta riba fitowa ne kamar sau biyu a mako, saboda la’akari da irin labaranta, wadanda ba kowane zai iya sayen ta kullum ba, sannan kuma mai karatu ba zai so ya rasa ba, saboda muhimmancin ta gare shi.

Har ila yau ya kuma jinjinawa Babban Daraktan kamfanin jaridar Mista Sam Nda Isiah, bisa hangen nesansa da tunanin da ya yi na hada kai da jami’ansa wajen canja tsarin fitowar jaridar wacce idan ta cigaba, za ta iya zama zakarar jaridun Hausa a tarayyar basar nan.

Sannan sai ya yi addu’ar Allah Ya bara daukaka wannan gidan jarida da yiwa al’ummar Najeriya, musamman ’yan Arewa murna na samuwar ingantacciyar jaridar Hausa a Najeriya wacce ta ke yin labarai da yaren da su ka fi magana da shi.

Exit mobile version